Yadda mutum 48 suka mutu bayan kifewar kwale-kwale a Sokoto

Asalin hoton, Ahmad Aliyu Sokoto/X
- Marubuci, Mansur Abubakar
- Aiko rahoto daga, Abuja
- Marubuci, Chukwunaeme Obiejesi
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Pidgin
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 7
Kimanin mutum 48 ne suka mutu yayin da ake ci gaba da neman yara 12 bayan haɗarin jirgin ruwa da ya faru a yankin Goronya da ke jihar Sokoto.
Akasarin waɗanda lamarin ya rutsa da su yara ne waɗanda ke kan hanyar zuwa gona a safiyar jiya Alhamis.
A tattaunawarsa da BBC, ɗan majalisar tarayya mai wakiltar Gada da Goronyo a majalisar wakilan Najeriya Bashir Gorau ya ce a halin yanzu masu ninkaya na ci gaba da aikin ceto domin ganin ko za a samo sauran yaran da suka ɓace da ransu.
"Akasarin waɗanda abin ya rutsa da su yara ne da mata, yara ƴan ƙasa da shekara 10," a cewar Gorau.
"Rafi ya raba mutanen ƙauyen da gonakinsu, shi ya sa a kodayaushe mutane ke amfani da kwale-kwalen katako domin zuwa gona," kamar yadda ɗan majalisar ya yi ƙarin haske.
Kifewar kwale-kwale na ci gaba da zama ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke jawo asarar rayuka a Najeriya, musamman a yankunan da ake amfani da koguna ke a matsayin hanyar sufuri ta yau da kullum.
Sau da dama idan irin hakan ta faru, hukumomi kan yi kira ga masu amfani da kwale-kwale su bi ƙa'idojin da suka dace. Sai dai galibi a kan yin watsi da irin waɗannan gargadi.
Ana ganin cewa rashin kayan aiki da ƙarancin hanyoyin sufuri ne ke tilasta wa mutane ci gaba da amfani da kwale-kwale a yanayi mai haɗari.
A baya-bayan nan kuma, jami'an ceto na ci gaba da neman waɗanda suka ɓace bayan wani kwale-kwale na katako ya kife a jihar Jigawa.
An yi ƙiyasin cewa mutane 40 ne ke a cikinsa, mafi yawansu mata manoma da ma'aikatan gona, lokacin da ya kife a ranar Lahadi.
Ya zuwa yanzu, an ceto mutane 23 da ransu, yayin da aka gano gawarwakin mutum tara daga cikin kogin.

Asalin hoton, Ahmed Ambali / BBC
Me ya sa ake yawan samun kifewar kwale-kwale?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
A watan da ya gabata, mutane 12 ciki har da mace mai juna biyu da ƙananan yara shida suka mutu bayan wani kwale-kwale ya kife da su a Kogin Benue da ke tsakiyar Najeriya.
A farkon wannan shekarar ma, mutum 14 sun rasu a Gumbi da ke jihar Kebbi lokacin da kwale-kwalensu ya kife yayin da suke rakiyar amarya.
A wannan shekarar kawai sama da mutum 55 sun mutu sakamakon kifewar kwale-kwale a sassa daban-daban na ƙasar, yayin da har yanzu ba a gano gawarwakin wasu da dama ba.
Ga miliyoyin ƴan Najeriya musamman mazauna karkara, koguna ne hanya mafi sauƙi wajen zirga-zirgarsu. Saboda ƙarancin gadoji da lalacewar hanyoyi, kwale-kwalen katako ne kaɗai hanyar da mutane ke amfani da ita wajen zuwa kasuwanni, ziyartar ƴan'uwansu ko gudanar da sauran harkokin yau da kullum.
Isiyaka Bello na ɗaya daga cikin waɗanda ibtila'in ya shafa. A bara ya rasa matarsa bayan kwale-kwalen da take ciki ya kife a jihar Kebbi tare da wasu mutum takwas.
Ya ce har yanzu bai warke daga raɗaɗin rashin matar ba.
"Ta bar min yara huɗu, kuma har yanzu ina ƙoƙarin rainonsu ni kaɗai. Duk lokacin da na ga ruwa, ita kawai nake tunawa."
Manyan abubuwan da ke haddasa haɗurran kwale-kwale sun haɗa da:
- Cunkoso a cikin kwale-kwale.
- Amfani da kwale-kwalen da ba su da inganci.
- Rashin bin ƙa'idojin tsaro, musamman sanya rigar kariya.
Duk lokacin da aka samu wani haɗarin kwale-kwale, hukumomi kan yi alƙawarin ɗaukar matakai, amma sau da dam ba a ganin wani gagarumin sauyi.
Mallam Sala Altine, Sarkin Ruwan Shiroro a jihar Neja, ya ce babban ƙalubalen da suke fuskanta shi ne ƙarancin rigunan ceto.
Ya ce yawancin kwale-kwalen da ke aiki a yankinsu na ɗaukar sama da fasinjoji 100, amma a mafi yawan lokuta ba sa samun rigunan kariya da suka wuce guda 10, ko ma ƙasa da haka.
"Muna son mu tabbatar da cewa duk wanda zai shiga kwale-kwale ya sanya rigar ceto. Amma ba za mu iya tilasta hakan ba, saboda ba mu da isassunsu."
Ya ƙara da cewa bayan wani haɗari da ya yi sanadin mutuwar kusan mutum 13, gwamnati ta yi alƙawarin samar da ƙarin rigunan ceto, amma abin da aka kawo daga baya bai wadatar ba.
A cewarsa, abin yana matuƙar ɓata masa rai ganin yadda fasinjoji ke shiga kwale-kwale ba tare da wata kariya ba.
Sakaci da rashin bin ƙa'idoji na taka rawa

Asalin hoton, Getty Images
Tafkin Shiroro da ke jihar Neja na daga cikin wuraren da aka fi samun munanan haɗurran kwale-kwale a Najeriya.
Kogin Neja, wanda shi ne na uku mafi tsawo a Afirka, na ratsawa ta jihar Neja, inda ƙananan rafuka da hanyoyin ruwa da dama ke haɗuwa da shi, lamarin da ya sa haɗurran kwale-kwale suka fi yawa a yankin.
Tsakanin watan Janairun 2023 da Oktoban 2025, jihar Neja ta kasance cikin jihohin da suka fi yawan mace-mace sakamakon kifewar kwale-kwale. Wani rahoto ya nuna cewa mutum 253 ne suka mutu a jihar tsakanin Yunin 2023 da Agustan 2025, cikin kusan mutum 860 da suka mutu a irin waɗannan haɗurra a faɗin ƙasar.
Wani mazaunin yankin ya ce, "Ba za a ce waɗannan haɗurra ƙaddara ce kawai ba. Sakaci ne da aka daɗe ana yi."
Sai dai daraktan yaɗa labarai na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) a jihar Neja, Ibrahim Husseini, ya ce gwamnati na ci gaba da raba rigunan kariya, amma mutane da dama da suka taso a yankunan da ke bakin ruwa kan yi watsi da amfani da su.
Ya shaida wa BBC cewa: "Akwai mutanen da aka haifa kuma suka tashi a yankunan bakin ruwa, suna ganin ba sa buƙatar sanya rigar kariya. Wasu kuma suna ganin ba ta musu daɗi, don haka wani lokaci yana da wuya a tilasta musu amfani da ita."
A yawancin al'ummomin da ke bakin ruwa, maza da dama sun iya iyo, amma mata ba su da yawa waɗanda ke da wannan ƙwarewar, lamarin da ke ƙara jefa su cikin haɗari idan kwale-kwale ya kife. Kuma su ne galibi ke zuwa bukukuwa kamar ɗaurin aure ko kuma kai amfanin gona kasuwa.

Matakan da gwamnati ke ɗauka
Bayan wani mummunan haɗarin kwale-kwale da ya kashe aƙalla mutum 32 a jihar Neja a bara, Hukumar Kula da Hanyoyin Ruwa ta Ƙasa (NIWA) ta sanar da cewa sanya rigar kariya ta zama wajibi ga duk masu amfani da jiragen ruwa a faɗin Najeriya.
Hukumar ta kuma haramta ɗaukar fasinjoji daga wuraren da ba ta amince da su ba. Darakta Janar na NIWA, Bola Oyebamiji, ya ce jiragen ruwan za su riƙa ɗaukar fasinjoji ne kawai daga tashoshin da hukumar ta tantance kuma ta yi wa rajista.
Sai dai duk waɗannan ƙa'idoji ba sabbi ba ne. suna cikin Dokar Sufurin Ruwa da aka fara aiwatarwa tun watan Janairun 2023, amma ba safai ake bin su yadda ya kamata ba.
"Doka ta tanadi cewa duk wanda zai yi tafiya a kan babban ruwa kuma akwai waɗanda ba za su iya iyo ba, dole ne su sanya rigar kariya," in ji Timothy Iwuagwu, shugaban cibiyar ƙwararrun masu bayar da kariya ta Najeriya,
Sai dai ya ce babban ƙalubalen shi ne rashin aiwatar da dokokin.
Iwuagwu ya kuma ce yawancin masu tukin kwale-kwale ba su da horo ko lasisin aiki.
"Ya kamata matuƙan jirgin ruwa su fahimci yanayin ruwa, igiya ruwa da kwararar ruwa kafin a ba su damar yin aikin.
Ya ce ya zama dole a rubuta adadin fasinjojin da kowane jirgin ruwa zai iya ɗauka domin hana lodin da ya wuce ƙima, wanda yake cikin manyan abubuwan da ke haddasa kifewar kwale-kwale.
Ko a wuraren da ake da rigunan kariya kuwa, ya ce sau da yawa ba su da inganci, sannan fasinjoji da dama ba su san yadda ake sanya su yadda ya kamata ba.
A shekarar da ta gabata gwamnati ta bayyana ƙudurinta na daina amfani da tsofaffin kwale-kwalen katako, amma Iwuagwu ya ce hakan zai ɗauki lokaci.
Ya ce abin da ya fi muhimmanci a yanzu shi ne tabbatar da ana bin dokokin da ake da su tare da bai wa ƙwararrun masana damar taka rawa wajen tsara matakan kare lafiyar masu amfani da hanyoyin ruwa.
An kuma ƙaddamar da jami'an kula da tashoshin ruwa domin hana lodin da ya wuce ƙima, amma Ibrahim Husseini na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (NSEMA) ya ce adadin jami'an bai isa ya yi tasiri dukkan tashoshin ruwa ba.
Wani ƙalubalen kuma shi ne yadda bishiyoyi da kututturansu suke kan wasu hanyoyin duk da ana sare dazuka. Husseini ya ce hakan na faruwa ne saboda rashin aikin tona hanyoyin ruwa yadda ya kamata.
Ya kuma bayyana cewa cire bishiyoyi daga hanyoyin ruwa ba aikin gwamnatin jiha ba ne, hukumar NIWA mai kula da hanyoyin ruwa na cikin gida ne ke da alhaki

'Mu huɗu ne kawai muka tsira cikin 40'
Shahararren mawaƙin Hausa, Aminu Bagwai, na daga cikin mutane huɗu kacal da suka tsira daga wani mummunan hatsarin kwale-kwale da ya kashe mutum 36 a jihar Kano shekaru 18 da suka wuce.
Cikin wata hira da BBC ya babu wani daga cikin fasinjojin da ke cikin kwale-kwalen a lokacin da hatsarin ya faru da ya saka rigar kariya.
Bayan wannan ibtila'in, ya rubuta wata waƙa da harshen Hausa mai suna "Ruwan Bagwai", wadda ta yi fice sosai tare da sanya mutane a duk faɗin arewacin Najeriya tausayawa abin da ya faru da shi.
Sai dai ya bayyana baƙin cikinsa cewa duk da an ɗauki shekaru, har yanzu ana ci gaba da samun haɗurran kifewar kwale-kwale a Najeriya.
"Har yanzu ina tunanin abin da ya faru a kullum, kuma abin baƙin ciki ne ganin har yanzu ana samun haɗurran kwale-kwale da ke jawo asarar rayuka."
"Fatana shi ne ya zama na ƙarshe," in ji shi.










