Abin da muka sani kan 'hukumar bogi' da aka ware wa kuɗi a kasafin Najeriya

Asalin hoton, Prince Adeniyi Adeyemi/Instagram
Wata sabuwar ce-ce-ku-ce ta kaure daga fadar shugaban Najeriya, yayin da ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasar, da kakakin shugaban ƙasar, Bayo Onanuga suka musanta iƙirarin da wani mutum mai suna Prince Adeniyi Adeyemi ya yi cewa Shugaba Tinubu ya naɗa shi shugaban wata hukuma.
Cikin iƙirarin nasa, Adeniyi Adeyemi, ya ce shugaban ƙasa ne ya naɗa shi matsayin shugaban kwamitin shugaban ƙasa kan shawarwarin tattalin arziki.
To sai dai, wata sanarwa da Femi Gbajabiamila, shugaban ma'aikatan fadar shugaban ƙasa ya fitar, ta ce gwamnatin Najeriya ba ta da wannan hukuma, kuma Shugaba Tinubu bai taɓa naɗa Adeyemi wani muƙami ba.
Sai kuma a ranar Laraba, Bayo Onanuga kakakin shugaban ƙasar ya sake fitar da wata sanarwa da a ciki yake musanta naɗin Adeyemi da ma musanta wanzuwar hukumar da yake iƙirarin jagoranta.
To sai binciken BBC ya gano cewa ma'aikatar da Adeyemi ya yi iƙirarin jagoranta ta samu kason kuɗi a kasafin 2026, duk da rashin wanzuwarta da fadar shugaban ƙasar ke iƙirari.
Haka kuma BBC ta gano hukumar ta gudanar da wasu manyan al'amuran gwamnati.
Onanuga ya zargi Adeyemi da amfani da takardun jabu ɗauke da sa hannu da hatimin shugaban ƙasa na bogi da ke nuna naɗinsa a ofishin da babu shi a doka.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ya ƙara da cewa ƴansanda sun fara bincike game da lamarin, yayin da ya ce hukumar da Adeyemin ke iƙirarin shugabanta ta bogi ce.
"Abin da ya faru da Prince Adeniyi Adeyemi Matthew ya yi kama da yadda wasu ke ƙirƙirar shafin intanet na bogi domin damfarar jama'a'', in ji Onanuga.
Onanuga ya ce ba wannan ne karon farko da Adeyemi yake iƙirarin jagorancin da ba a naɗa shi ba.
"A watan Nuwamban 2016 ya taba ayyana kansa a matsayin jakada kuma shugaban Ƙungiyar Matasa ta Duniya (WYO), da ke ƙarƙashin Majalisar Dinkin Duniya...kuma kafofin yaɗa labarai sun riƙa ɗaukar sa a hakan, har zuwa lokacin da MDD ta ƙaryata wanzuwar ƙungiyar,'' in ji Onanuga.
To sai dai Adeyemi ya musanta duka zarge-zargen da Onanuga da Gbajabiamila suka yi masa.
A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar 26 ga watan Yunin 2026, ya ce yana da sahihan takardun da ke tabbatar da cewa Shugaba Tinubu ne ya naɗa shi muƙamin.
Adeyemi ya ce hukumar da yake jagoranta na da asusun ajiya a babban bankin ƙasar CBN, kuma gwamnati ta ware wa hukumar kuɗi a kasafin kuɗin 2026.
"Mu ƙaddara abin da suke faɗi gaskiya ne cewa babu wannan hukuma, to ta yaya har aka ware mata kuɗi a kasafin 2026, a shafi na 50 da 51 na kundin kasafin?'' kamar yadda ya yi tambaya.
"Wannan ba batu ne na wata manufa ta ƙashin kai ba, batu ne na ruɗanin da yake buƙatar amsa," in ji shi.
Adeyemi ya yi kira ga shugaban ƙasa ya kafa kwamiti mai zaman kansa da zai binciki lamarin tsakaninsa da Gbajabiamila.
"Dalilin hakan shi ne fayyace wa mutane gaskiya. Ba wani batun musantawa ba. Idan na yi ba daidai ba, kwamitin binciken ya tabbatar. Idan kuma Gbajabiamila ne da gaskiya duka dai kwamitin ya tabbatar," kamar yadda ya yi ƙarin haske.
BBC ta duba shafin intanet na ofishsin da ke kula da kasafin kuɗin ƙasar, kuma sun tabbatar da gaskiyar cewa hukumar ta PFIPC ta samu kaso a kasafin, inda sunan hukumar ya bayyana a shafi na 50 da na 51 na kasafin 2026
A cewar Onanuga, bayan binciken ƴansanda ya samu Adeyemi da laifi an kai shi ƙara babbar kotun tarayya, wadda za ta fara zama ranar 27 ga watan Yuli.

Asalin hoton, PFIPC/Instagram
Wane ne Prince Adeniyi Adeyemi?
Kafin yanzu babu wani cikakken bayani a bayyane game da Prince Adeniyi Adeyemi, in ban da kasancewarsa shugaban hukumar PFIPC da aka fi sani da kwamitin shugaban ƙasa kan shawarwarin bunƙasa tattalin arziki..
Hukumar ta ayyana kanta a matsayin cibiyar gwamnati a shafin Instagram wadda ke "aiwatar da haɗin gwiwa don janyo masu zuba jari daga ƙetare zuwa Najeriya''.
Bisa ga bayanan shafin na Instagram, an buɗe shi ne a 2025, kuma adireshin hukumar na yanar gizo: www.pfipc.gov.ng ba ya tafiya lokacin da muke haɗa wannan labari.
To sai dai wannan Adeniyi Adeyemi ba shi ne Prince Akeem Adeniyi Adeyemi, ɗanmajalisar wakilan Najeriya ba, suna dai da suna iri ɗaya ne.
Me ƴan Najeriya ke cewa?
Ƴan Najeriya da dama sun riƙa muhawara kan batun, inda wasunsu ke bayyana batun da abin kunya ga fadar shugaban ƙasar.
Fitaccen lauyan nan na ƙasar, kuma ɗan gwagwarmaya, Femi Falana ya ce kamata ya yi Shugaba Tinubu ya kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin bincikar lamarin, musamman da batun ya haɗa da shugaban ma'aikatar fadar shugaban ƙasar.
Falana ya ce bai kamata fadar shugaban ƙasar ta ce ta wanke Gbajabiamila ko duk wani da ke da hannu a lamarin ba.
"Ya kamata fadar shugaban ƙasar ta miƙa wa hukumar ICPC ragamar binciken Gbajabiamila da sauran mutane da ke da hannu a cikin lamari, saboda a ciki akwai zarge-zargen da suka shafi damfara da cin hanci,''
"Ya kamata gwamnati ta yi wa ƴan ƙasa bayanin ta yaya aka ware wa hukumar bogi kuɗi a kasafin 2026, sannan ta yaya har ta samu asusu a Babban Bankin Ƙasar, CBN''?
Haka shi ne tsohon sanatan Kaduna Shehu Sani ya wallafa a shafinsa na X cewa ya taba riƙe muƙamin mataimakin shugaban kwamitin harkokin waje na Najeriya, kuma bai taɓa ganin wata hukuma da wannan suna ba.







