Me ya sa matsalar tsaron Najeriya ta ƙi ƙarewa duk da kuɗin da gwamnati ke kashewa?

Asalin hoton, OHN WESSELS/AFP via Getty Images
- Marubuci, Adesola Ikulajolu
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News Pidgin
- Aiko rahoto daga, Lagos
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
Daga wannan gwamnati zuwa waccan, a kowace shekara kason da ake ware wa fannin tsaro a kasafin kudi shi ne ke da kaso mafi yawa. To amma me ya sa aka kasa shawo kan matsalar tsaron?
Wannan ita ce tambayar da galibin 'yan Najeriya da kuma masana tsaro ke yi tsawon shekaru yayin da rashin tsaro ke kara kamari a kasar.
Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da Naira Tiriliyan 49.7 ga majalisar dokoki a zaman kasafin kudi na shekara ta 2025, kuma daga cikin wannan adadin, Naira Tiriliyan 4.91 duk kason fannin tsaro ne.
A kasafin kudin shekara ta 2026 wanda ya kai Naira Tiriliyan 58.18, fannin tsaro ne ke da kaso mafi yawa na Naira Tiriliyan 5 da biliyan 41
A watan Afrilun 2026, Shugaba Tinubu ya rattaba wa dokar kasafin kuɗi 2026 din hannun abin da ya bayar da bayanin yadda za su kashe kudaden, kuma duk fannin tsaron ne ke da ka kaso mafi yawa.
Sai dai duk da shekarun da aka kwashe sojoji na kai hare-hare, da kari a kason fanni tsaro a kasafin kudi, da kuma wasu matakai da gwamnati ke dauka, rashin tsaro ya ci gaba da zama daya daga ciki kalubalai mafiya girma da Najeriya ke fuskanta.
Sace dalibai da malamai na baya-bayan nan da aka yi a jihohin Borno da Oyo, ya saka jama'a nuna shakku na gaske da yin zanga-zanga suna neman amsar wai tsowa wane lokaci Najeriya za ta dauka kafin ta shawo kan matsalar tsaro?
Matsalar tsaro a Najeriya
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Daga satar dalibai zuwa tayar da bam, daga kai hare-hare kan kauyuka da wuraren ibada zuwa kashe manyan jami'an soja, matsalar tsaro a Najeriya na ci wa mutane da yawa tuwo a kwarya.
Kungiyoyi hudu dake kai hare-hare a Najeriya kuma suke da alaka da alqaida su ne: Boko Haram da JNIM, da Ansaru da kuma Mahmudawa.
Akwai kuma wasu kungiyoyi biyu da ke da alaka da ISIS wato ISWAP da Lakurawa su ma suka kai hare-hare a cikin kasar.
Kasancewar wadannan kungiyoyin 'yan ta'adda ne ya jawo kai manyan hare-haren da ake kai wa a arewacin Najeriya.
Amma a baya-bayan nan, tun bayan hawan shugaba Tinubu kan Mulki, an kai manyan hare-haren a yankin kudu, abin da ke jama'a ke tambayar me yake faruwa ne kuma me ke haddasa wadannan manya hare-hare da sace-sacen jama'a?
A shekarar 2025, Shugaban Najeriyar ya ayyana dokar ta-baci a duk fadin kasar bayan kwashe makonni ana samun tashe-tashen hankulan a sassan kasar daban-daban.
A wani bangare na dokar, shugaban ya umarci rundunonin soji da 'yansanda da suka kara daukar sabbin jami'ai.
Amma a cikin wannan lokacin, an samu hare-haren 'yan ta'adda da 'yan fashin daji a sassa daban-daban na kasar.
Har ya zuwa yau, wasu daga cikin daliban da aka sace ba su dawo gida ba duk da shekarun da wadannan 'yan ta'addan suka kwashe suna karbar kudin fansa.
Me ya sa har yanzu Najeriya ke fama da matsalar tsaro?
Wani rahoton ya ce abubuwan ke sa wadannan 'yan bindigar yin abin da suke yi su ne bukatu na akida, da siyasa da kuma yanki.
Wani rahoton kuma da kamfanin SB Morgan ya fitar y ace 'yan Najeriya sun biya masu garkuwa da mutane akalla dala Miliyan 1.66 tsakanin watan Yuli na 2024 da kuma watan Yuni na 2025, abin da ya sa garkuwa da mutanen ta zama safara mai kawo kudi sosai a kasar.
Masana sun ce karbar kudin fansa na daya daga cikin dalilan da suka sa 'yan ta'adda ke kai wa mutane hari tare da yi garkuwa da su a Najeriya.
Suka ce mutane kan mutu a cikin wadannan hare-hare kuma 'yan fashin dajin kan kashe mutanen da iyalansu suka kasa biyan kudin fansa.
Dr. Buhari Ubandawaki wani kwararren kan bincike da sanyan ido, wanda ke da gogewa ta tsawon shekaru na aiki da kungiyoyin da ba na gwamnati ba, ya bayyana wasu dalilai da dama da suka haddasa karuwar hare-haren 'yan fashin daji da kuma Boko Haram a Najeriya. Ya ta'allaka karuwar hare-haren ga kwadayin samun kudi da kuma matsin lamba daga sojoji.
"Abin da ke yi wadannan masu aikata laifuka kaimi shi ne kudin fansar da suke samu daga garkuwar da suke yi da mutane; shi ya sa suke kara kaimi wajen kai hare-hare kan kauyukka, da matafiya da wuraren ibada da kuma makarantu."
Ya kara da cewa, su kuma 'yan ta'dda suna da manufa ta dogon lokaci da suke son cimma kuma duk hare-haren da suke kai wa suna yi ne don yada akidarsu, don haka idan Najeriya na son samun galaba a kansu ko kuma rage musu karfi to dole ne ta rika amfani da bayanan sirri.
Game da batun yadda rundunar soji ke kashe kudaden da ake ware ma ta da kuma yadda ake samun karuwar hare-hare a Najeriya, Group Kyaftin Sadiq Garba, wani tsohon jami'in sojan Najeriya ya shaidawa BBC cewa wajibi ne a rika bin Kadin yadda ake kashe kudaden da ke warewa fannin tsaro.
Garba ya ce ba wai kawai amince da kasafin kudin fannin tsaro kawai ke da muhimmanci ba, ya zama wajibi hukumomin da abin ya shafa su rika sa ido domin tabbatar da ana amfani da kudin da ake ware wa fannin na tsaro a hanyar da ta da ce.
"Ba wanda ke tababa game da kishin kasa da kuma rikon amanar hafsoshin tsaro, amma maganar it ace yak ama su rika sa ido yadda ya kamata. Saboda wasu lokutta, kudaden na iya shiga inda bai kamata su shiga ba."
"Idan bas u tsara kasafin kudin yadda ya kamata ba, ba zai ishe su b a. Daya daga cikin matsalolin su ne kodayaushe muna maganar kasafin kudi, kason yana dayawa, to amma a ina ake kashe kudaden? Inji Kyaftin Garba mai ritaya.
Wani batun da tsohon jami'in soji ya yi shi ne ko ana bincikar kudaden da ake warewa fannin tsaro domin tabbatar da ko ana kashe su wajen yin abin da aka ware su domin sa.
"Idan 'yan majalisar dattawa ba su shirya wa bincikar idan ake kashe kudaden ba to akwai matsala, ba a haka dukkan manyan kasashe. Ka bincika a Amurka ko Burtaniya, duk idan aka bai wa mutane kudaden al'umma to dole ne a saka musu ido ko a bincike su."
Ya ce idan Najeriya na so magance matsalar tsaro a kasar to dole duka gwamnati da majalisar dokoki su tashi tsaye wajen sa ido da bincike, a maimakon kara kason da ake ba fannin tsaro a kowace shekara ba tare da samun biyan bukataba.
Me ya kamata gwamnati ta yi?
Domin shawo kan wannan matsalar, masanin kan harkokin tsaro, Dr. Buhari Ubandawaki, y ace matsalolin tsaron Najeriya yanzu suna bukatar matakai masu yawa da za a aiwatar a lokaci daya domin tunkarar 'yan ta'adda.
Ya ce dole gwamnati ta toshe hanyoyin da suke samun makamai. Saboda ta nan 'yan fashin dajin ke samun karfin kai hare-hare.
"Ba za a iya cin galaba kan 'yan ta'adda bas ai an toshe kafofin da suke samun makamai."
Ya ce kamata ya yi gwamnati ta yanke manyan hanyoyin shigo da haramtattun makamai cikin kasar kuma ta inganta matakan tsaron iyakoki.
Da ma Ministan tsaron Najeriya, Christopher Musa, ya ce akwai yiwuwar Najerya ta gina bango kan iyakokinta da wasu kasashe domin tabbatar miyagun mutanesun daina shiga kasar yadda suka ga dama.
A cikin wata hira da BBC, Mr. Musa ya ce akwai kasashen da iyakokinsu sun na Najeriya,amma sai da suka yi suka samu tsaro. Idan aka yi hakan to za hana kungiyoyin 'yan ta'adda da na 'yan fashin daji shigo da makamai a cikin kasar.







