Yadda matsalar daba ke ƙara ƙamari a Kano

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Al'ummar wasu unguwanni a jihar Kano da ke arewa maso yammacin Najeriya, na ci gaba da kokawa kan yadda matsalar daba da amfani da makami ke ci gaba da zama babbar barazana.

Al'ummar unguwannin da suka hada da Ɗan Agundi da Sabuwar Ƙofa, da Ƙofar Nasarawa, da Ƙofar Mata, da unguwar Gini na cikin wuraren da matsalar ta fi muni.

Wani mazaunin unguwar Sabuwar Kofa da ke cikin karamar hukumar Birni, ya shaida wa BBC cewa irin yadda suke fama da rikicin Daba da yadda matsalar da haddasa musu asara da dama.

Ya ce,"Tun shekara biyu zuwa uku da suka wuce ba mu taba samun hutu ba tare da 'yan daba sun shigo mana unguwa sun yi sare-sare da jefe-jefe kai har ma yanke-yanke, ga kuma jiwa mutane ciwo ko kisa ma a wani lokaci wanda kuma ba su ji ba su gani ba."

"Duk gilasan gidajenmu a fashe suke, kuma abin takaicin ma shi ne um a unguwarmu ba mu da mutum guda da za a ce dan daba ne, unguwarmu ita ce mahadarsu, kuma sun fi zuwa wajen karfe 10 na dare, sannan kuma a irin wannan fada da suke na fasa motoci sun fi 60, ban da asarar rayuka da aka yi." In ji shi.

Matsalar daba a sassan birnin Kano ta kai matsayin da zai yi wahala a shafe kwanaki uku baka ji an yi arangama tsakanin 'yan dabar wannan unguwa da waccan unguwar ba.

Kuma matsalar fadan Dabar ba wai kawai rikici ne tsakaninsu ba, rigimar na shafar wadanda ba su ji ba su gani ba.

Wani mutum da irin wannan fada ya rutsa da shi, ya shaida wa BBC cewa, shi fa da tuni ya rasa ransa a irin wannan fada.

"Na taba burma mini wuka a ciki na, Allah ne ya yi da sauran numfashi na, don sai da dauki tsawon lokaci kafin na warke bayan na yi mini aiki." In ji shi.

Shi ma wani mutum da BBC ta zanta da shi a unguwar Kofar Nasarawa, ya ce, cikin kwanaki goma da suka gabata, kwana biyu biyu ne kacal, yan dabar ba su auka musu ba a unguwarsu.

Ya ce," Wannan bala'i na daba ya damu jama'a, yanzu idan zabe yazo yadda daba ke kara kamari, ya za'ayi ke nan? Gaskiya ya kamata gwamnati ta kara himma wajen yin abin da ya kamata domin kawo karshe fadan daba."

A baya-bayan nan 'yan daba sun aikata kashe-kashe musamman a tarukan siyasa da tare tituna su hana wucewa saboda fadan iyaka da kai munanan hare-hare tsakar dare a wasu unguwanni tare da aukawa 'yan kasuwa.

Abin da yasa ake ci gaba da kiraye-kirayen a kawo karshen matsalar tun kafin ta fi karfin al'umma.

Rikicin daba na cikin manyan matsalolin tsaro da ke sanadin rayukan ɗaiɗaikun mutanen da basu ji-ba-basu-gani-ba a tituna da gidaje a birnin na Kano duk da ikirarin da hukumomi ke yi na aikin magance matsalar.