Barazana 10 da AI ke yi wa ɗan'adam

..

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Fasahar ƙirƙirarriyar basira ta AI na iya amfanar ɗan'adam matuƙa, fiye da yadda rayuwa take a baya kafin fara amfani da fasahar ta AI.

Ƙwarraru a harkar fasaha sun ce idan aka yi amfani da AI cikin hikima da yadda ya kamata to fasahar za ta iya taimakawa wajen inganta rayuwar ɗan'adam, bunƙasa tattalin arziki, da warware wasu daga cikin manyan ƙalubalen da duniya ke fuskanta.

To sai dai kuma masanan sun fara kokawa kan yadda AI ke tattare da manyan haɗurra ga rayuwar dan'adam.

Ko a wannan makon ma sai dai babban jami'in Majalisar Dinkin Duniya mai kula da Haƙƙin Ɗan Adam, Volker Türk, ya yi gargaɗin cewa tasirin kirkirarriyar basira ta AI na iya zama "barazana ga wanzuwar bil'adama".

Yayin da yake jawabi ga Majalisar Ɗinkin Duniya a Geneva ranar Litinin, Mista Türk ya yi kira da a ɗauki matakin gaggawa a matakin ƙasa da ƙasa, tare da ƙarfafa matakan kariya da suka shafi wannan fasaha.

Ya ce ya kamata gwamnatoci da kamfanonin fasaha su ɗauki mataki tun kafin ci gaban basirar ya gagari kundila.

To dangane da wannan batu BBC ta tattauna da Muhammad Ubale Kiru, wani masanin fasahar ta AI, kuma malami a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria kuma ya fito da wadansu barazana guda 10 kamar haka:

Barazanar AI 10 ga ɗan'adam

..

Asalin hoton, Getty Images

  • Rashin Ayyukan yi

AI na iya sarrafa ayyukan da a baya mutane ke yi, wanda hakan zai iya rage buƙatar ma'aikata a fannoni kamar masana'antu, hidimar kwastomomi, sufuri, da harkokin gudanarwa.

  • Yaɗa ƙarya da son zuciya
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

AI na iya ƙirƙirar rubuce-rubuce, hotuna, sauti, da bidiyoyi na bogi masu kama da na gaskiya, wanda ke sauƙaƙa yaɗa labaran ƙarya, zamba, ko rinjayar ra'ayin jama'a.

  • Tauye sirrin jama'a

Tsarin AI na iya tattarawa da nazartar bayanan sirri masu yawa game da mutane, wanda ke haifar da damuwa kan sa ido, bibiyar mutane ba tare da izini ba, da kuma rasa sirrin bayanai.

  • Son kai da wariya

Idan an horar da AI da bayanan da ke ɗauke da son kai ko wariya, za ta iya yanke hukunci marasa adalci a fannoni kamar ɗaukar ma'aikata, bayar da bashi, aikin 'yan sanda, ko kiwon lafiya, tare da ƙara tsananta rashin daidaito da ake da shi.

  • Barazanar tsaron intanet

Masu aikata laifuka na iya amfani da AI wajen ƙaddamar da hare-haren intanet, ƙirƙirar dabarun damfara masu inganci, gano raunin tsarin kwamfuta, da haɓaka shirye-shiryen kwamfuta masu cutarwa.

  • Makamai masu cin gashin kansu

Amfani da AI a harkokin soja na iya haifar da makamai da za su iya zaɓar da kuma kai hari ba tare da cikakken sa hannun ɗan'adam ba, wanda ke tayar da damuwar ɗabi'a da tsaro.

  • Rashin ikon Ɗan'adam

AI mai matuƙar ƙwarewa na iya yanke shawarar da mutane ba sa fahimta gaba ɗaya. Idan babu isassun matakan kariya, ayyukanta na iya saɓawa manufofi da ƙimar ɗan'adam.

  • Rashin daidaito a tattalin arziƙi

Fa'idodin AI na iya taruwa a hannun wasu ƙalilan na kamfanoni, gwamnatoci, ko mutane, wanda zai iya ƙara giɓin arziƙi da iko tsakanin masu yawa da masu kaɗan.

  • Dogaro da AI fiye da kima

Yawan dogaro da AI na iya rage ƙwarewar mutane, tunani mai zurfi, da ikon yanke shawara da kansu a tsawon lokaci.

  • Barazanar nan gaba ga bil'adama

Wasu masana suna gargaɗin cewa idan AI mai matuƙar ci gaba ta zarce ɗan'adam sosai wajen iya aiki, kuma ba a tabbatar tana aiki da manufofin ɗan'adam ba, za ta iya haifar da manyan haɗurra ga bil'adama a nan gaba.

Tarihin AI

An fara kafa tushen fasahar Artificial Intelligence wato AI ne a shekarar 1956, lokacin da aka gudanar da taron bincike mai suna Dartmouth Summer Research Project on Artificial Intelligence a kwalejin Dartmouth College, Amurka.

A wannan taro ne masanin kimiyya John McCarthy ya ƙirƙiri kalmar"Artificial Intelligence", wadda ake amfani da ita har zuwa yau.

Sai dai kafin gudanar da taron Dartmouth a 1956, a 1950, Alan Turing ya wallafa takardar bincike mai suna Computing Machinery and Intelligence, inda ya gabatar da tambayar ko na'ura za ta iya yin tunani kamar mutum. Wannan ya kafa tubalin binciken AI.

Daga 1960s zuwa 1980s: An fara samar da shirye-shiryen kwamfuta da ke kwaikwayon wasu dabarun tunanin ɗan'adam.

A shekarun 1990s zuwa yau kuma cigaban kwamfuta, manyan bayanai , da hanyoyin koyon na'ura sun haifar da babban ci gaba a AI.