An rantsar da shugaban kasa biyu a Guinea-Bissau

Umaro Sissoco Embalo

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Umaro Sissoco Embalo tsohon firai minista ne kuma Janar din soja
An wallafa

Rikici ya kaure bayan an rantsar da shugaban kasa biyu a Guinea-Bissau inda manyan jam'iyyun siyasar kasar ke ikirarin samun nasara a zaben shugaban kasar.

Tsohuwar jam'iyya mai mulki a kasar ta nada shugaban kasa na rikon kwarya tare da rantsar da sabon firai minista, duk da cewa ta fadi a zaben shugaban kasar na bara.

Ita kuma jam'iyyar PAIGC ta daukaka kara zuwa Kotun Kolin kasar tana neman a ba ta nasarar zaben - amma kotun bata riga ta yanke hukunci ba.

Yanzu kasar na da shugaban kasa biyu da firai minista biyu daga jam'iyyu daban-daban.

Shugaban jam'iyyar adawa, Umaro Sissoco Embalo, wanda ya samu fiye da kashi 50 na kuri'un da aka jefa a zaben na ikirarin cewa shi ne halastaccen shugaban kasar.

A ranar Alhamis ne Mista Embalo ya rantsar da kansa a matsayin shugaban kasa a wani otal.

Jam'iyyar PAICG - wadda ta mamaye fagen siyasar Guinea-Bissau tun bayan samun 'yanci kasar a 1974 - ba ta da ko daya daga cikin wadanda aka ba wa shugaban kasar ko firai minista.

Ita ma ta nada shugaban 'yan majalisarta Cipriano Cassamá, a matsayin shugaban kasa. Amma ba shi ne dan takararta a zaben na watan Disamba ba.

Cipriano Cassamá

Asalin hoton, Dan Sanha

Bayanan hoto, Jam'iyyar PAIGC ta rantsar da Cipriano Cassamá a matsanin shugaban rikon kwarya

Guinea-Bissau na yawan fama da rikice-rikice, inda aka gudanar ko kuma aka yi yunkurin yi juyin mulki har sau tara a kasar daga shekarar 1980.

Masu fasakwaurin miyagun kwayoyi na yawan amfani da kasar a matsayin hanyar jigilar kwayoyinsu daga Kudancin Amurka zuwa kasashen nahiyar Turai.