KAI TSAYE, Abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya 27/06/2026

Wannan shafi ne da ke kawo muku abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Asabar 27 ga watan Yunin 2026.

Taƙaitattu

Skip Bidiyo and continue reading
  • xxx
  • Ummulkhairi Aliyu
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • xxx
  • Arsenal
  • xxx
  • xxx

Rahoto kai-tsaye

Daga Aisha Babangida

  1. Labarai da dumi-dumi, Adadin waɗanda suka mutu a girgizar ƙasar Venezuela ya kai 1,430

    Wani gini

    Asalin hoton, Reuters

    Hukumomin Venezuela sun ce adadin waɗanda suka mutu sakamakon girgizar ƙasar ya kai 1,430.

    Wani jigo a majalisar dokokin kasar, Jorge Rodriguez ne ya bayyana haka ta gidan talbijin na ƙasar.

    Har yanzu masu aikin ceto na ci gaba da zaƙulo gawarwaki daga cikin baraguzan gine-gine da suka rufta

    Tuni dai kasashen duniya ke ci gaba da aikewa da tawagogin masu aikin ceto domin taimakawa aikin ceton rayukan

    A cikin makon nan ne Venezuela ta fukanci mummunar girginzar ƙasar da ba a taɓa ganin irinta ba cikin shekaru a ƙasar.

  2. An kama wasu mutum 7 da ake zargin ƙusoshin Boko-Haram ne a filin jirgin Katsina

    Olubunmi Tunji-Ojo

    Asalin hoton, Olubunmi Tunji-Ojo/X

    Hukumomin Najeriya sun ce an kama wasu mutum bakwai da ake zargi da kasancewa jiga-jigan a ƙungiyoyin Boko-Haram da ISWAP ne.

    Ministan cikin gida na ƙasar, Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana haka lokacin sanya hannu kan sabuwar dokar shaidar ɗan ƙasa a Abuja.

    Mista Tunji-Ojo ya ce an kama mutanen ne a lokacin d asuka dawo naga aikin Hajji na 2026 a filin jirin saman Katsina cikin makon da ya gabata.

    Ministan ya ce an kama mutanen ne bayan bibiyar bayanan mutanen da suka tafi aikin hajji a faɗin ƙasar.

    Ya ce yanzu haka mutanen bakwai na hannun hukumar tsaro ta DSS wadda take gudanar da bincike kan lamarin.

  3. Za a samu katsewar lantarki a Kano da wasu jihohin Arewa ranar Lahadi

    Lantarki

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar rarraba wutar lantarki ta Najeriya TCN ta ce za a gudanar da wani aikin gyaran cibiyar raba wutar lantarki da ta shafi Kano da wasu jihohin arewacin kasar a ranar Lahadi 28 ga watan Yunin 2026.

    Cikin wata sanar da daraktan ya da labaran hukumar, Ndidi Mbah ya fitar ya ce za a gudanar da gyaran domin inganta aikin rarraba wutar lantarkin.

    Ya ce katsewar za ta shafi aikin rarraba wutar kamfanonin KEDCO da wasu ɓangarorin kamfanin rarraba wuta na Jos (JEDC) da na Yola (YEDC) da na Yobe (YEDC) da ke samar da wuta ga kwastominsa na Kano da Katsina da Jigawa da kuma garin Azare na jihar Bauchi.

    Sauran garuruwan da matsalar za ta shafa sun haɗa da Nguru na jihar Yobe da garin Gazaoua na Jamhuriyar Nijar.

    TCN ta kuma nemi afuwar al'umomin waɗannan yankuna tare da alkawarta cewa za a maida wutar da zarar an kammala aikin.

  4. Kotun Iran ta ce mawaƙiya Parastu Ahmadi da aka yankewa hukunci za ta iya ɗaukaka ƙara

    ....

    Asalin hoton, youtube.com/@ParastooAhmadii

    Hukumar yaɗa labarai ta bangaren shari’a a Iran ta bayyana cewa hukuncin da aka yanke wa mawakiya Parastu Ahmadi da wasu mutum takwas ba shi ne na ƙarshe ba, tana mai cewa har yanzu suna da damar daukaka ƙara bisa doka.

    A baya-bayan nan ne kotu a lardin Qom ta yanke musu hukuncin bulala 74, tare da hana su fita ƙasashen waje da kuma hana su gudanar da ayyukan waƙa na wani lokaci.

    A kwanakin baya ne aka bayyana cewa kotu ta yankin Qom ta yanke wata fitacciyar mawaƙiya a Iran hukuncin bulala 74 bayan da ta yi wasa ba tare da sanya hijabi ba, wanda wajibi ne a ƙasar

    Bidiyonta ya karaɗe shafukan sada zumunta har ya zama abin magana a ƙasar.

    Bayan fitar bidiyon, hukumomin shari’a sun dauki matakin shigar da kara kan wadanda suka shirya taron, tare da rufe wurin tarihi na Dirgchin caravanserai inda aka gudanar da wannan kade-kade.

  5. Iran ta buƙaci Iraq ta ɗauki mataki kan ƙungiyoyin Kurdawa masu adawa dake ƙasarta

    Gwamnatin Iran ta buƙaci Iraq da ta ɗauki matakin gaggawa kan kasancewar wasu ƙungiyoyin Kurdawa masu adawa da ita a yankin Kurdistan na ƙasar a cewar rahotanni daga kafofin yaɗa labarai.

    A cikin wata wasiƙa da aka aika ta hanyar jakadan Iraq a Tehran, Yasser al-Hajjaj, ta nuna cewa Iran na son gwamnatin Iraq da ta yankin Kurdistan su kama shugabannin waɗannan ƙungiyoyi su miƙa su ga Iran, ko kuma su aika da su zuwa wata ƙasa ta uku cikin wani takamaiman lokaci.

    Sai dai kawo yanzu, babu wata martani daga gwamnatin Iraq, yankin Kurdistan ko kuma ƙungiyoyin Kurdawan da abin ya shafa kan wannan batu.

    Wannan na zuwa ne bayan yarjejeniyar tsaro da Iran da Iraq suka ƙulla a shekara ta 2022, wadda ta tanadi hana amfani da yankin Kurdistan wajen kai hare-hare kan Iran.

    Lamarin ya sake ta’azzara ne yayin da aka samu rikice-rikicen fada a kusa da birnin Baneh, inda wasu sojoji suka mutu, yayin da ƙungiyar PJAK ta zargi rundunar IRGC da amfani da jirgin maras matuki wajen kai hari tare da barazanar mayar da martani idan harin ya ci gaba.

  6. INEC na shirin cire NDC daga rajistar jam’iyyun siyasa bayan hukuncin kotu

    ....

    Asalin hoton, INEC/X

    Hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC) na shirin cire jam’iyyar NDC daga jerin jam’iyyun da ta amince da su, bayan wani hukuncin Kotun Tarayya da ya soke umarnin da ya tilasta mata yin rajistar jam’iyyar a baya.

    INEC ta bayyana cewa ta nemi kwafin hukuncin kotun (CTC), inda ta ce za ta aiwatar da abin da kotu ta yanke da zarar ta samu shi.

    Ta ƙara da cewa kafin hukuncin da aka yanke a watan Disambar 2025, ta riga ta ƙi amincewa da buƙatar NDC na yin rajista a matsayin jam’iyya.

    Alƙalin Kotun Tarayya da ke Lokoja, Mai Shari’a Isah Dashen, ne ya soke hukuncin da aka yanke a baya, inda aka umarci INEC ta yi wa NDC rajista.

    Yanzu ana sa ran komawa kotun domin sake sauraron shari’ar kafin a yanke hukunci na ƙarshe.

  7. Amnesty ta buƙaci hukumomin Najeriya sun binciki kisan shugaban makiyayen Benue

    ....

    Asalin hoton, Amnesty International/Facebook

    Ƙungiyar Amnesty International ta bukaci hukumomin Najeriya da su gudanar da bincike cikin gaggawa da gaskiya kan kisan gilla da aka yi wa shugaban ƙungiyar makiyaya a jihar Benue, Alhaji Ardo Risku, tare da wani abokinsa.

    Ƙungiyar ta bayyana damuwarta kan yadda halartar wani taron sulhu ya zama sanadin mutuwa, tana zargin cewa hukumomin yankin sun kasa daukar matakin da ya dace don hana aukuwar wannan lamari.

    Binciken da ƙungiyar ta gudanar ya nuna cewa an gayyaci marigayin ne ranar Juma’a 26 ga Yunin 2026 domin halartar wani taron tsaro da ƙaramar hukumar Ohimini ta shirya, amma bayan kusan sa'a guda da barin wurin, shi da abokinsa suka faɗa hannun wasu mutane a ƙauyen Okudu, inda aka kashe su bayan an harbe su sau da dama.

    Ƙungiyar ta ce hotunan gawarwakin da ta gani sun nuna irin mummunan halin da aka tsinci gawarwakinsu a ciki, inda ta ƙara da cewa wannan kisan ya faru ne mako guda bayan an kai hari ga daya daga cikin ‘ya’yan marigayin, wanda aka ji masa raunuka masu tsanani.

    Amnesty International ta jaddada cewa dole ne a binciki lamarin ba tare da ɓata lokaci ba, tare da gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

    Ta kuma buƙaci a tabbatar an samar wa iyalan waɗanda aka kashe damar samun adalci da diyya.

  8. Idan Amurka ta sake kai mana hari, za mu mayar da martani mafi muni – Iran

    ....

    Asalin hoton, Tasnim news agency

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta gargaɗi Amurka cewa za ta fuskanci martani mai tsanani idan ta sake kai hare-hare, bayan abin da ta bayyana a matsayin harin da Amurka ta kai kan gaɓar tekunta.

    A wata sanarwa da IRGC ta fitar, ta zargi Amurka da kai hare-haren sama kan wasu wurare a gaɓar tekun Iran, lamarin da ta ce ya biyo bayan farmakin da aka kai kan wani jirgi a mashigar ruwan Hormuz, wanda Iran ke ganin ya bi hanyar da ba ta halatta ba.

    Iran ta ce wannan mataki na Amurka ya sabawa yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma alƙawuran da ta ɗauka, tana mai jaddada cewa hakan ya sa ta ɗauki mataki na mayar da martani.

    Sai dai IRGC ba ta bayyana cikakken bayani kan wuraren da aka kai hare-haren ko irin ɓarnar da aka samu ba, amma ta ce kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz na karkashin alhakinta ne bisa wasu yarjejeniyoyi.

    A ƙarshe, Iran ta sake jaddada cewa idan aka sake yin irin waɗannan hare-hare, martanin da za ta mayar zai fi tsauri, abin da ke nuna ƙarin tsanantar rikici a yankin.

  9. Za a dawo da zirga-zirgar jirage tsakanin Iran da UAE

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Hukumar kula da Filin Jirgin Sama na Imam Khomeini a Iran ta sanar da cewa ana sa ran dawo da zirga-zirgar jiragen sama tsakanin kasar da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) nan da karshen wannan mako.

    Shugaban kamfanin, Ramin Kashifazar, ya ce kamfanonin jiragen saman cikin gida sun riga sun kammala shirye-shiryen sake buɗe hanya zuwa Dubai, ɗaya daga cikin mahimman hanyoyin zirga-zirga a yankin.

    Ya kuma bayyana cewa ana ci gaba da tattaunawa da kamfanonin jiragen sama na kasashen waje, inda ake sa ran musamman kamfanonin ƙasashe makwabta za su fara komawa aiki cikin ƙanƙanin lokaci.

    Dangane da Lufthansa kuwa, Kashifazar ya ce kamfanin ya nuna aniyarsa na dawo da ayyukansa a Iran, sai dai ya yi nuni da cewa hakan zai iya ɗaukar lokaci saboda kamfanoni kan sauya tsare-tsarensu idan aka dakatar da wata hanya.

  10. NDLEA ta ƙwace miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai naira biliyan 5 a Rivers

    ....

    Asalin hoton, NDLEA/x

    Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeirya (NDLEA) ta ce ta ƙwace miyagun ƙwayoyi da darajarsu ta kai kusan Naira biliyan 5 a tashar jiragen ruwan Onne da ke jihar Rivers.

    Kwamandan NDLEA a tashar, Omerio Odo, ne ya bayyana hakan yayin bikin ranar yaƙi da ta’ammali da miyagun ƙwayoyi ta duniya a 2026.

    Ya ce kayayyakin da aka kama sun haɗa da kwantena guda bakwai ɗauke da sama da kwayoyi miliyan 3.5 na opioids da kuma kwalabe miliyan 1.2 na codeine, tare da kayan da nauyinsu suka kai ton 206.

    Ya ƙara da cewa an samu wannan nasara ne ta hanyar tattara bayanan sirri, ƙara tsauraran matakan sa ido da kuma haɗin gwiwa da sauran hukumomin tsaro da masu ruwa da tsaki a harkokin jiragen ruwa.

    Odo ya bayyana cewa kayayyakin da aka kama kaya ne da za su shafi rayuwar mutane da iyalai da kuma al’umma baki ɗaya. Ya kuma yi gargaɗin cewa duk da muhimmancin tashar Onne wajen kasuwanci, masu safarar miyagun ƙwayoyi na ƙoƙarin amfani da hanyoyin ruwa wajen shigo da haramtattun kaya cikin ƙasar.

    Kwamandan ya tabbatar da cewa NDLEA za ta ci gaba da ƙara ƙaimin matakai ba ƙaƙƙautawa wajen daƙile fataucin miyagun ƙwayoyi, tare da jaddada buƙatar haɗin kai daga gwamnati, al’umma da hukumomi.

    Ya kuma bukaci masu harkokin dakon kaya da su riƙa bincika kayayyaki sosai tare da bayar da rahoton duk wani abu da ake zargi.

  11. An gurfanar da ƙarin mutum 17 kan kisan matar da aka ƙona a Kaduna

    ....

    Asalin hoton, Family

    Rundunar ƴansandan jihar Kaduna ta sanar da gurfanar da wasu ƙarin mutane 17 da ake zargi da hannu a kisan gayyan da aka yi wa wata mata a Ungwar maraban Jos, na jihar Kaduna a makon da ya gabata.

    Wata sanarwar da ta fito daga ofishin jami'in hulɗa da jama'a na rundunar DSP Mansir Hassan ta ce an gurfanar da waɗanda ake zargin ne yayin da ake ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.

    Sabarwar ta ƙara da cewa bayan kammala binciken farko, an gurfanar da wasu mutane talatin da uku (33) da ake zargi da laifin haɗa baki da kuma yin taro ba bisa ƙa’ida ba.

    Rundunar ta kuma bayyana cewa mutane talatin (30) da aka kama bayan aukuwar lamarin, ba same su da hannu wajen aikata laifin ba, kuma an sake su ba tare da wani sharaɗi ba.

    Rundunar ta sake nanata cewa ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin, inda ta bayar da tabbacin cewa ta na ƙara ƙaimi wajen ganowa da kamo duk waɗanda ke da hannu, ko kuma suka taimaka wajen aikata wannan laifi.

  12. Iran ta zargi Amurka da ƙeta yarjejeniya bayan hare-haren soji

    ....

    Asalin hoton, Getty Images

    Ma’aikatar Harkokin Wajen Iran ta bayyana hare-haren da Amurka ta kai a matsayin “karya yarjejeniya a fili,” tana mai cewa hakan ya ci karo da yarjejeniyar da aka ƙulla tsakanin ƙasashen biyu domin kawo karshen yaki.

    A cikin wata sanarwa, ma’aikatar ta ce harin da Amurka ta kai a gaɓar tekun Iran” ya saɓawa Mataki na 2, Sashe na 4 na Yarjejeniyar Majalisar Ɗinkin Duniya, tare da ƙeta Sashe na 1 na Yarjejeniyar fahimtar juna kan kawo karshen yaki da aka sanyawa hannu a ranar 18 ga Yuni..

    Haka kuma, Iran ta bayyana harin da Isra’ila ta kai a Lebanon a matsayin “keta yarjejeniya” tana mai ɗora alhakin sakamakon abubuwan da ke faruwa kan Amurka da sauran ɓangarorin da ta ce suna da hannu wajen goyon bayan matakan da Amurka ke ɗauka kan Iran.

    A daren jiya, rundunar sojin Amurka (CENTCOM) ta sanar da cewa jiragen yaƙinta sun kai hari kan rumbunan makamai masu linzami da jiragen yaƙi marasa matuƙa na Iran, da gabar teku.

    Bayan waɗannan hare-hare, Rundunar IRGC ta Iran ta ce ta mayar da martani ta hanyar kai hari kan wuraren da sojojin Amurka ke jibge a yankin.

  13. Adadin mutanen da suka mutu a girgizar ƙasar Venezuela ya haura 900

    ...

    Asalin hoton, Reuters

    Mahukunta a Venezuela sun ce adadin mutanen da suka mutu sakamakon girgizar ƙasa biyu masu ƙarfi da suka afku a ranar Laraba ya haura mutum 900, yayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutane 50,000 har yanzu ana nemansu ba a same su ba.

    A yammacin ranar Juma’a kuma, an ji wata sabuwar girgizar ƙasa mai matsakaicin ƙarfi a tekun arewacin Venezuela.

    Cibiyar Nazarin Girgizar Ƙasa ta Euro-Mediterranean (EMSC) ta ce karfin girgizar ya kai maki 4.9.

    Shaidu sun ce an ji girgizar a babban birnin ƙasar, Caracas, da kuma birnin Maracay da ke arewa.

    Dubban mutane na ci gaba da karɓar magani sakamakon raunukan da suka samu daga girgizar ranar Laraba, inda da dama daga cikinsu ke kwance a asibitocin wucin-gadi.

    Gine-gine da dama a arewacin Venezuela, ciki har da Caracas, sun lalace ko kuma sun rushe sakamakon waɗannan girgizar ƙasa, lamarin da ya ƙara tsananta halin da ake ciki yayin da ake ci gaba da aikin ceto waɗanda suka maƙale a ƙarƙashin ɓaraguzai.

  14. Jami’an Iran sun soki sanarwar ƙasashen Gulf kan goyon bayan Amurka

    Jami’an Iran sun ci gaba da mayar da martani mai tsauri ga sanarwar da Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Gulf (GCC) ta fitar wadda ta nuna damuwa kan matakan Iran a yankin tare da jaddada goyon baya ga tsaron ƙasashen Gulf da kuma alaƙa da Amurka.

    Shugaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dokokin Iran, Ebrahim Azizi, na daga cikin jami’an da suka mayar da martani, inda ya gargaɗi ƙasashen membobin ƙungiyar da cewa, “nuna goyon baya ga tsarin Amurka zai lalata tsaro da kwanciyar hankalinku ne kawai.”

    Azizi ya kuma bayyana cewa “ƙarfin makamai masu linzami da jiragen yaki marasa matuƙa da kuma kula da mashigar ruwan Hormuz,” su ne manyan abubuwan da Iran da ba za ta bari a ƙetare ba.

    Duk da cewa Iran ba ta tabbatar ko ƙaryata harin da aka kai kan wani jirgin dakon kaya a jiya ba, Azizi ya jaddada cewa, “hanya ɗaya tilo da za a tabbatar da tsaron yankin ita ce nesanta kai da Amurka.”

    Kalaman shugaban kwamitin tsaron majalisar sun biyo bayan martanin wasu jami’an Iran da dama kan sanarwar da ƙasashen GCC suka fitar.

    .

  15. Mun kai hari kan sansanonin sojin Amurka a yankin Gabas ta Tsakiya - Iran

    ...

    Asalin hoton, IRNA

    Rundunar juyin juya halin Iran (IRGC) ta bayyana cewa rundunar ruwanta ta kai hari kan wasu wuraren da sojojin Amurka ke jibge a yankin Gabas ta Tsakiya, a matsayin martani ga hare-haren da Amurka ta kai a gaɓar tekun Iran.

    A wata sanarwa da sashen hulɗa da jama’a na IRGC ya fitar, ta ce Amurka ta kai hare-haren sama kan gaɓar tekun Iran bayan ta kai farmaki kan wani jirgi a mashigar ruwan Hormuz, bisa hujjar cewa jirgin yana bi ta wata hanya da Iran ke ganin “ba ta da izini.”

    IRGC ta bayyana hare-haren a matsayin ƙeta yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma alƙawuran da Amurka ta ɗauka.

    Sai dai sanarwar ba ta yi ƙarin bayani kan inda aka kai hare-haren ba, ko irin makaman da aka yi amfani da su, da kuma irin ɓarnar da aka yi.

    Haka kuma, sanarwar ta ce bisa ga Mataki na 5 na Yarjejeniyar Islamabad, kula da zirga-zirgar jiragen ruwa a mashigar Hormuz na karkashin alhakin Iran ne.

    IRGC ta gargaɗi Amurka cewa idan aka sake kai hare-hare, Iran za ta mayar da martani mafi tsanani.

  16. Assalamu alaikum!

    Masu bibiyar shafin labaran kai tsaye na BBC Hausa,Barkanmu da Safiyar ranar Asabar.

    Kamar kodayaushe, za mu kawo maku labarai game da abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya.

    Aisha Babangida ce ke fatan kasancewa da ku a daidai wannan lokacin.

    Za ku iya leƙawa shafukanmu na sada zumunta na facebook da X da kuma whatsapp domin karanta wasu labaran da kallon bidiyo da ma tafka muhawara.

    Ku kasance tare da mu.