'Dalilinmu na rufe sansanin 'yan gudun hijira na Bama'

'Yan gudun hijira

Asalin hoton, AFP

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 3

Gwamnatin jihar Borno ta bayyana dalilanta na bayar da umarnin a hanzarta rufe sansanin 'yan gudun hijira da ke garin Bama, wanda shi ne mafi girma a wajen birnin Maiduguri.

Gwamnatin ta bakin mai magana da yawun gwamnan jihar, Dauda Iliya, ta shaida wa BBC cewa, ana yawan samun karuwar aikata miyagun laifuka a sansanin, da fargabar da ake yi, na ƴan bindiga na shiga sansanin suna sace ƴan gudun hijirar, da kuma zargin da ake na yadda wasu mutanen gari ke komawa sansanin don samun tallafi.

Dauda Iliya ya ce," Ko wa ya san rayuwa a sansanin 'yan gudun hijira bata da dadi, sannan ayyukan masha da dama na faruwa a sansanin misali shaye-shaye da sauran muggan laifuka, kuma yawanci matasa ne ke aikata irin laifuka."

Ya ce," Wani dalilin rufe sansanin, shi ne idan har kana zaune a sansanin 'yan gudun hijirah to mutum ba zai samu damar da gudanar da sana'arsa ba har ya dogara da kansa."

" Idan aka zugunnar da 'yan gudun hijira a waje guda ko aka mayar da su garuruwansu to za su samu damar yin sana'a da noma da kiwo da sauran harkokin kasuwanci." In ji shi.

Mai magana da yawun gwamnan na Borno, ya ce, " Sansanin 'yan gudun hijira na Bama shi ne na 22 da aka rufe a jihar, sannan mutanen da ke zaune a sansanin su kimanin dubu fiye da dubu 30 an mayar da su garuruwa daban-daban har biyar."

Ya ce," Mutanen da ke wannan sansanin sai da aka basu zabin garin da suke so su zauna a cikin garuruwa biyar din, kuma suka zaba sannan aka mayar da su, kuma sai da gwamnati ta samar da abubuwa da dama kafin a mayar da su."

" Gwamnati ta samar da shemomi a garuruwan da aka mayar da 'yan gudun hijirar, sannan na gina gidaje a wasu daga cikin garuruwan, don haka duk wadanda za su koma garuruwan za su kasance suna gida ko shemar da za su zauna, ga kuma kudi har naira dubu 100 da za a bawa kowane magidanci daga cikin 'yan gudun hijirar, matansu kuma naira dubu 50." In ji shi.

Dauda Iliya ya ce," An kuma basu kayan abinci da suka hada da shinkafa da masara da kuma wasu kayayyaki kamar bargo da katifa da kayan sawa duk a bawa kowane iyalai da aka kwashe daga sansanin na Bama."

Ya ce, " Dangane da batun tsaro kuwa a inda aka tsugunnar da wadannan mutane na karfafa matakan tsaro sosai kuma sai da su kansu jami'an tsaron suka tabbatar da cewa za a ajiye mutane a garuruwan sannan aka mayar da su, ga sojoji a wuraren dama sauran jami'an tsaro."

Mai magana da yawun gwamnan ya kuma ce nan da wani lokaci ma za a rufe sansanin da ke Gwoza.