Chelsea ta dage kan Lacroix, Newcastle na harin Nmecha

Asalin hoton, Getty Images
Ana sa ran ɗan wasan bayan Crystal Palace Maxence Lacroix zai koma Chelsea kan fam euro miliyan 55 (Fam miliyan 47.4), bayan da ɗan wasan ya takawa Faransa Leda a gasar cin kofin duniya da ke yi. (L'Equipe - in French)
Newcastle United na zawarcin ɗan wasan Borussia Dortmund da Jamus Felix Nmecha, cikin jadawalin ƴan wasan da za su ɗauka a kakar nan. (Mail)
Newcastle ta yi watsi da tayin da Arsenal ta yi wa ɗan wasan Brazil Bruni Guimareaes. (ESPN)
Shugaban Tottenham Roberto de Zerbi na son ɗauko mai tsaron ragar Antonin Kinsky, cikin jerin ɗan wasan da zai dauko, yayin da suke son siyar da mai tsaron ragar Italiya Guglielmo Vicario, 29. (Teamtalk)
Manchester United da Chelsea sun bi sahun Arsenal wajen zawarcin ɗan wasan Uruguay Maxi Araujo, daga Sporting. (Record - in Portuguese)
Ɗan wasan Italiya Marco Palestra, ya shirya kamala komawar tasa Chelsea daga Atlanta, bayan ya ganin likita a London.(Football Italia)
Ɗan wasan Marseile Mason Greenwood da ke son komawa Roma, maimakon Fnerbahce ko Al-Hilal, inda ƙungiyar da ke Italiya ke son taya ɗan wasan kan euro miliyan 50 (Fam miliyan 43.1). (Corriere dello Sport - in Italian)
AC Milan ta amince da ta ɗauko dan wasan Protugal da Paris St-Germain Goncalo Ramos, da tuni aka duba lafiyar sa. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Atlanta United ta tuntuɓi Atletico Madrid kan yiwuwar ɗaukar dan wasan Sipaniya Koke. (Marca - in Spanish)
Ajax na harin ɗauko mai tsaron ragar Jamus Marc-Andre ter Stegen, daga Barcelona. (Mundo Deportivo - in Spanish)










