Cameroon da Malawi: Yau za a kafa sabon tarihi a ƙwallon mata a Afirka

Asalin hoton, CAF Women’s Football and TotalEnergies Africa Cup of Nations
A yau, Lahadi 16 ga Agusta 2026 ne za a buɗe sabon babi a tarihin ƙwallon ƙafar mata a Afirka, inda Cameroon da Malawi za su fafata domin lashe kofin na gasar ta bana.
Abin da ya fi ɗaukar hankali shi ne cewa duk wacce ta yi nasara za ta daga babban kofin gasar nahiyar ne a karon farko.
Wannan ya sa ake kallon wasan a matsayin mai muhimmanci saboda tarihin da ake dako.
Gasar, wadda Najeriya ta mamaya na tsawon lokaci, ya zo da ba-zata a bana, inda duk kusan ƙasashen nahiyar masu ƙarfi aka yi waje da su.
Daga cikin ƙasahen da suka fi ƙoƙari a gasar ta mata, akwai Najeriya wadda ta lashe gasar sau 10, sai Equatorial Guinea mai biyi, sai Afirka ta Kudu mai ɗaya tilo, sannan akwai kuma akwai ƙasar Morocco mai masaukin baƙi.
Rawar da Malawi taka zuwa yanzu
Tafiyar Malawi a wannan gasar ta kasance ɗaya daga cikin manyan labaran da suka fi jan hankali saboda wannan karon farko.
Amma tun daga wasan farko suka aikawa da saƙon cewa ba su zo Morocco domin wasa ba, inda suke doke Nigeria da ci 3-2. Wannan nasara ta ba su ƙarfin gwiwa, sannan suka ci gaba da taka rawar gani har zuwa yanzu.
A wasan kusa da na ƙarshe kuma, Malawi ta doke Algeria da ci 3-1, inda Tabitha Chawinga ta taka muhimmiyar rawa da ƙwallo biyu.
Daga cikin ƴanwasan da suka fi ɗaukar a hankali a gasar akwai ƴan'uwa mata Tabitha da Temwa Chawinga.
Temwa Chawinga ce ke kan gaba wajen neman takalmin zinare da ƙwallo biyar, sannan ta taimaka aka zuwa biyu.
Kamaru
Ita kuwa Kamaru za a iya cewa ta samu nasarar zuwa wasan ƙarshe ta hanyar ba-zata.
Da farko dai tawagar ba ta samu gurbin shiga gasar ba a tsaron farko na ƙasashe 12, sai da aka faɗaɗa ne zuwa 16 ta samu dama.
Sai dai sun yi amfani da wannan damar sosai, inda tun bayan gasar suke taka rawar gani zuwa wasan ƙarshe.
Daga cikin wasannan da Kamaru ta yi bajinta akwai doke Morocco mai masauƙin baƙi a bugun fanareti, inda golar tawagar Michaely Bihina mai shekara 22 ta zama gwana.
Wasan ƙarshe
A gefe guda akwai Malawi, wacce ta dogara sosai kan saurin kai hari, kuzari da ƙwarewar 'yan'uwa biyu.
A ɗayan ɓangaren kuma akwai Cameroon, wacce ta nuna cewa za ta iya jure matsin lamba, ta kare raga sannan ta jira damar da za ta iya canza wasa.
Tambayar da za a yi ita ce: Shin harin Malawi zai iya karya lagon tsaron bayan Cameroon, ko kuwa tsaron Cameroon zai daƙile hare-haren Malawi?
Kamaru da Malawi dai duk suna neman abin da ba su taba samu ba: kofin na WAFCON.
Ga Malawi, wannan dama ce ta mayar da gasar farko ta zama tarihi wasan ƙasar na har abada.
Ita kuma Kamaru, nasara za ta zama ɗoriya a kan alfarmar da ta samu ta zuwa gasar.
Za a buga wasan na ƙarshe na Kamaru a Malawi ranar da misalin ƙarfe 10:00 na dare agogon Gabashin Afirka.










