Kana amfani da shafin BBC mai bayyana rubutu kawai (babu hoto) domin rage cin data. Idan ana so a ga hotuna da bidiyo sai a koma babban shafinmu.
Kamaru ta lashe kofin mata na Afirka a karon farko
Kamaru ta lallasa Malawi da ci 3-0 a wasan ƙarshe, wanda hakan ya ba ta damar lashe kofin gasar kofin ƙwallon ƙafa ta mata ta Afirka a karon farko.
Marie Ngah Manga ce ta sanya Kamaru a gaba tun a minti na 20 da fara wasa bayan ta jefa ƙwallo da kai, sai kuma ƴar wasa Naomi Eto ta jefa ƙwallo ta biyu a minti na 30 bayan fara wasa a karawar da aka yi a birnin Rabat na ƙasar Moroko.
Haka nan Naomi ta jefa ƙwallo na uku bayan minti uku da dawowa daga hutun rabin lokaci, lamarin da ya cike ƙwallo uku cif da suka bai wa Kamaru nasar.
Duk da haka Malawi ta taka rawar gani, ganin cewa ita ce ƙasar da aka fi kallo a matsayin mafi rashin ƙwarewa a tsakanin tawagogin ƙasashen Afirka da suka halarci gasar ta 2026, wadda take a matsayi na 153 a duniya a jerin ƙasashen da ke taka ƙwallon mata.
Za a iya cewa Kamaru ta samu nasarar zuwa wasan ƙarshe ta hanyar ba-zata.
Da farko dai tawagar ba ta samu gurbin shiga gasar ba a tsarin farko na ƙasashe 12, sai da aka faɗaɗa zuwa 16 ta samu dama.
Sai dai sun yi amfani da wannan damar sosai, inda tun bayan fara gasar suke taka rawar gani har ta kai ga ƙasar ta lashe kofin.
Daga cikin wasannan da Kamaru ta yi bajinta akwai doke Morocco mai masauƙin baƙi a bugun fanareti, inda golar tawagar Michaely Bihina mai shekara 22 ta zama gwana, sannan kuma ta cire Najeriya, wadda ita ce ƙasar da ta fi kowace lashe kofin a tarihi.
Rawar da Malawi taka
Tafiyar Malawi a wannan gasar ta kasance ɗaya daga cikin manyan labaran da suka fi jan hankali saboda wannan karon farko.
Amma tun daga wasan farko suka aika da saƙon cewa ba su zo Morocco domin wasa ba, inda suke doke Nigeria da ci 3-2. Wannan nasara ta ba su ƙarfin gwiwa, sannan suka ci gaba da taka rawar gani har zuwa wasan ƙarshe.
A wasan kusa da na ƙarshe kuma, Malawi ta doke Algeria da ci 3-1, inda Tabitha Chawinga ta taka muhimmiyar rawa da ƙwallo biyu.
Daga cikin ƴanwasan da suka fi ɗaukar a hankali a gasar akwai ƴan'uwa mata Tabitha da Temwa Chawinga.