Me ya janyo sabon takun saƙa tsakanin Turkiyya da Isra'ila?

..

Asalin hoton, Reuters

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Turkiyya ta yi Allah-wadai da harin da aka kai wa sansanin soji a Syria, Isra'ila ta zargi Syria da bai wa Turkiyya mafaka.

Turkiyya ta yi Allah-wadai da harin da aka kai kan sansanin soji na Abu Duhur da ke lardin Idlib a arewa maso yammacin Syria, bayan hare-haren sama da suka lalata filin jirgin da ma'ajiyar makamai.

Isra'ila ba ta fito kai tsaye ta amince da alhakin kai harin ba, amma ta zargi Syria da karya yarjejeniyar tsaro da ke tsakaninta da Isra'ila ta hanyar bai wa dakarun Turkiyya damar kasancewa a sansanin.

A nata ɓangaren, Turkiyya ta bayyana kalaman ofishin Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu cewa lamarin na barazana ga tsaron Isra'ila a matsayin "marasa tushe".

Gidan talabijin na gwamnatin Syria ya ruwaito cewa hare-haren sama takwas da aka kai ranar Talata sun auka wa hanyoyin sauka da tashin jiragen sama da kuma wuraren ajiyar makamai na filin jirgin Abu Duhur. Rahotannin farko sun nuna cewa babu wanda ya rasa ransa ko ya jikkata.

Ko da yake Isra'ila ba ta bayyana kai tsaye ko ita ce ta kai harin ba, ta ce gwamnatin Syria na dab da karya matsayar tsaro da ke tsakaninsu ta hanyar amincewa da tura dakarun Turkiyya sansanin.

Sai dai Syria da Turkiyya duk sun ɗora alhakin harin kan Isra'ila, inda suka yi gargaɗin cewa irin wannan mataki na iya ƙara ruruta rikici a yankin.

Amurka ma ta yi tir da hare-haren da aka kai wa sansanin sojin, tana mai bayyana lamarin a matsayin "tsokanar da ba ta da amfani" wadda ka iya ƙara ƙamarin rikici a yankin.

A baya, Ma'aikatar Harkokin Wajen Syria ta bayyana harin da aka kai wa sansanin da ke Idlib a matsayin "mataki na cin zarafi da ba shi da wani dalili", tare da yin Allah-wadai da shi cikin kakkausar murya.

Ma'aikatar ta ce harin na barazana ga zaman lafiya da tsaron yankin Gabas ta Tsakiya, tare da kira ga ƙasashen duniya su ɗauki matakin hana ƙara tabarbarewar lamarin.

Martanin Turkiyya kan kalaman Isra'ila game da tura dakarunta zuwa Abu Duhur

..

Asalin hoton, Reuters

Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Bayan shafe yini guda jami'an Isra'ila ba tare da yin wani bayani a hukumance kan lamarin ba, ofishin Firaministan ƙasar Benjamin Netanyahu ya fitar da wata sanarwa inda ya ce Isra'ila da Syria sun amince da ci gaba da kiyaye tsarin tsaron da ke akwai, amma Syria na gab da karya wannan yarjejeniya bayan ta amince wa sojojin Turkiyya su kafa sansanin jiragen sama kusa da birnin Aleppo.

Turkiyya ba ta tabbatar da cewa tana shirin tura dakarunta zuwa sansanin sojin Abu Duhur da ke Syria ba. Sai dai ta yi watsi da ikirarin Isra'ila cewa kasancewar sojojin Turkiyya a wurin zai zama barazana ga tsaron Isra'ila.

A wata sanarwa da kamfanin dillancin labarai na gwamnati Anadolu ya wallafa, Sashen Sadarwa na Fadar Shugaban Ƙasar Turkiyya ya ce "Zarge-zargen marasa tushe da ofishin Firaministan Isra'ila ya yi na da nufin halasta hare-haren sama da Isra'ila ke kai wa kan ikon mallaka da cikakkiyar 'yancin kan ƙasar Syria."

Sansanin Abu Duhur na da nisan kusan kilomita 70 daga iyakar Turkiyya.

Ba a yi amfani da sansanin a matsayin filin jiragen yaƙi ba tun shekarar 2013. Ƙungiyoyin da ke adawa da gwamnatin tsohon shugaban Syria Bashar al-Assad sun karɓe ikon yankin a watan Disamban 2024 bayan hare-haren da suka kai a sassa daban-daban na ƙasar.

A halin yanzu gwamnatin Syria na ƙoƙarin sake gina wasu cibiyoyin soji da suka lalace a lokacin yaƙe-yaƙen da suka kai ga kifar da gwamnatin Assad.

Kungiyar Syrian Observatory for Human Rights ta ce hare-haren Isra'ila sun biyo bayan wata ziyara da tawagar sojojin Turkiyya ta kai sansanin a kwanakin baya, a wani yunƙuri na farfaɗo da ayyukan filin jirgin.

Sojojin Turkiyya sun kasance daga cikin manyan masu goyon bayan sabuwar gwamnatin Syria tun bayan kifar da Bashar al-Assad. Sai dai Isra'ila na ci gaba da kallon ƙarfafa alaƙar soji tsakanin Ankara da Damascus a matsayin abin damuwa ga tsaronta.

A cikin sabuwar sanarwar da ta fitar, Turkiyya ta jaddada cewa za ta ci gaba da haɗin gwiwarta da Suriya bisa abin da ta kira "ƙa'idojin da doka ta tanada".

A cikin watannin baya, Isra'ila ta kai hare-haren sama da dama a yankunan tsakiyar da kudancin Syria. Sai dai wannan harin na Abu Duhur na daga cikin kaɗan da suka shafi cibiyoyin gwamnatin Syria tun watan Maris, kuma ya faru ne a wani yanki mai nisa da kudancin Syria da Isra'ila ke cewa dole ne ya kasance kariya daga duk wata barazana ga yankinta.

Martanin Amurka da ba a saba gani ba: "Ba a gargaɗi Turkiyya ba"

Jakadan Amurka a Turkiyya kuma wakilin musamman na Shugaba Donald Trump kan harkokin Syria da Iraki, Tom Barrack, ya ɗauki matsayi da ba a saba gani ba ta hanyar bayyana damuwar Washington kan harin da Isra'ila ta kai wa sansanin sojin Abu Duhur da ke Syria.

Ya ce Amurka na ƙarfafa dukkan ɓangarorin da su fifita tattaunawa maimakon amfani da ƙarfin soja.

Barrack ya ce Amurka na matuƙar damuwa da hare-haren da Isra'ila ta tabbatar da kai wa sansanin, yana mai bayyana su a matsayin "tsokanar da ba ta da amfani" wadda ke ƙara rura wutar rikici maimakon taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya a yankin.

Ya kuma bayyana cewa ba a sanar da Turkiyya game da harin ba kafin a kai shi. A cewarsa, ya ga jiragen yaƙin Isra'ila suna dosar yankin da ke kusa da Turkiyya, lamarin da zai iya sa Ankara ta ɗauka cewa akwai yiwuwar a kai mata hari, ta kuma fara shirye-shiryen mayar da martani.

Barrack ya ce matakan kariya da aka ɗauka sun taimaka wajen hana lamarin rikidewa zuwa wata babbar arangama. Ya ƙara da cewa babban abin da Washington ta fi mayar da hankali a kai yanzu shi ne rage tashin hankalin tare da ƙarfafa ɓangarorin su yi taka-tsantsan.

Har ila yau, ya kare shugaban Syria na yanzu Ahmed al-Sharaa, wanda ya jagoranci dakarun adawa da gwamnatin Bashar al-Assad kafin ya hau mulki.

Barrack ya ce al-Sharaa bai ƙirƙiri ko kula da ƙungiyoyin mayaƙa ba, kuma ya sha bayyana muradinsa na rage rashin jituwar da ke tsakaninsa da Isra'ila.

Ya kuma bayyana cewa Amurka na ƙoƙarin samar da wata hanyar sadarwa tsakanin Isra'ila, Turkiyya da Syria domin kauce wa duk wani kuskuren fahimta da zai iya janyo rikici a gaba.

Ko da yake Turkiyya da Isra'ila sun kafa wata hanyar sadarwa ta tsaro a bara domin hana arangama tsakanin dakarunsu a Syria, rahotanni sun nuna cewa Ankara ba ta samu wani gargaɗi daga Isra'ila kafin kai harin na baya-bayan nan ba.

Tun bayan hawansa mulki, Ahmed al-Sharaa ya ƙara kusantar ƙasashen yamma, musamman Amurka. A baya ya kai ziyara fadar White House inda ya gana da Shugaba Donald Trump, a wani mataki da ke nuna sauyin alakar Damascus da Washington.