Arsenal na nazari kan Yildiz, Atletico na dab da kammala cinikin Jackson

Danwasan gaba na Juventus da Turkiya Kenan Yildiz

Asalin hoton, Getty Images

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 1

Arsenal na nazari kan ɗauko ɗanwasan gaba na Juventus da Turkiya Kenan Yildiz, mai shekara 21. (Independent)

Atletico Madrid na son kammala yarjejeniya kan ɗanwasan gaba na Senegal Nicolas Jackson, mai shekara 25 daga Chelsea. (Marca - in Spanish)

Manchester City na tattaunawa domin ɗauko ɗanwasan gaba na Brazil Allan Elias, mai shekara 22, daga Palmeiras. (ESPN)

Manchester City ta latsa Crystal Palace kan ɗanwasan tsakiya na Ingila Adam Wharton, mai shekara 22, amma an yi watsi da buƙatar. (Sun)

Tottenham na sa ido kan ɗanwasan gaba na Faransa Jean-Philippe Mateta, mai shekara 29 daga Crystal Palace. (Football Insider)

Inter Milan na son ɗanwasan gaba na Brazil Gabriel Martinelli, mai shekara 25 daga Arsenal. (Corriere dello Sport - in Italian)

AC Milan ta mayar da hankali kan ɗauko ɗanwasan baya kuma ɗanwasan Manchester City da Portugal Ruben Dias, mai shekara 29, take hari. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Ɗanwasan Bayer Leverkusen da Burkina Faso Edmond Tapsoba, mai shekara 27, ya zama ɗanwasan da Manchester United da Tottenham da Newcastle ke hari. (Teamtalk)

Ɗanwasan baya na Faransa Axel Disasi, mai shekara 28, na dab da zuwa Crystal Palace a matsayin aro daga Chelsea. (Sun)

Barcelona har yanzu ba ta tura bukatar ta ba kan ɗanwasan gaba na Argentina Lautaro Martinez, mai shekara 28, amma Inter Milan ba ta da niyyar rabuwa da ɗanwasan. (Gazzetta dello Sport - in Italian)

Barca na nazarin ɗauko ɗanwasan gaba na Spain Ayoze Perez, mai shekara 33 da kuma ɗan ƙasar Georgia Georges Mikautadze, mai shekara 25, da dukkaninsu ke murza leda a Villarreal. (Marca - in Spanish)