Zubimendi ka iya barin Arsenal, Madrid za ta tsawaita kwantiragin Guler

Asalin hoton, Getty Images
Ɗan wasan tsakiya na Sifaniya, Martin Zubimendi, na Arsenal mai shekara 27, na iya neman barin ƙungiyar a watan Janairu bayan rasa matsayinsa a cikin tawagar farko. Chelsea da Real Madrid na daga cikin ƙungiyoyin da ke sha'awar ɗaukarsa. (Teamtalk)
Tsohon ɗan wasan gaba na Argentina, Mauro Icardi, mai shekara 33, kuma wanda ba ya ƙarƙashin wata ƙungiya a yanzu, ya nuna cewa a shirye yake ya koma Everton bayan rabuwa da Galatasaray a watan Yuli. (Teamtalk)
Sai dai wasu majiyoyi a Everton sun susuntar da rahotannin da ke danganta ƙungiyar da Icardi da kuma tsohon ɗan wasan gaba na Faransa, Anthony Martial, mai shekara 30, wanda ya buga wa Monterrey ta Mexico wasa a karo na ƙarshe. (i Paper - subscription required)
Liverpool ta taɓa nuna sha'awar ɗan bayan Italiya Marco Palestra, mai shekara 21, kafin daga bisani ya koma Chelsea daga Atalanta, amma buƙatar ƙarfafa wasu sassan ƙungiyar ta hana Liverpool ci gaba da zawarcinsa. (i Paper - subscription required)
Real Madrid ta gabatar wa ɗan wasan tsakiyar Turkiyya Arda Guler, mai shekara 21, sabon kwantiragi na tsawon shekara shida. Ana kuma cewa kocin Chelsea, Xabi Alonso, na cikin masu sha'awar ɗan wasan. (Fabrizio Romano via Teamtalk)
Ɗan bayan Italiya Giorgio Scalvini, mai shekara 22, wanda ake dangantawa da Newcastle United, ya rattaba hannu kan sabon kwantiragi na tsawon lokaci da Atalanta. (Fabrizio Romano)
Aston Villa na tattaunawa da ɗan bayanta na Netherlands Ian Maatsen, mai shekara 24, kan sabon kwantiragi domin ci gaba da zamansa a Villa Park. (Football Insider, external)
Ɗan wasan gaba na Crystal Palace, Eddie Nketiah, mai shekara 27, na tunanin sauya ƙasar da yake buga wa kwallo daga Ingila zuwa Ghana. (The Standard)
Ɗan wasan gaba na Colombia Kevin Viveros, mai shekara 26, na gab da tsawaita kwantiraginsa da Athletico Paranaense, duk da sha'awar da Sunderland da Aston Villa suka nuna a kansa a lokacin bazara. (ESPN Brazil via Sunderland Echo)














