Wane ne Ibrahim Masari, kuma mene ne tasirinsa a jam'iyyar APC?

Asalin hoton, Alh. Ibrahim Kabir Masari/FB
- Marubuci, Muslim Muhammad Yusuf
- Aiko rahoto daga, BBC Hausa
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 6
A ƴan kwanakin nan, mutumin da sunansa ke yawan yawo, musamman a bakin ƴan jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya, shi ne Ibrahim Masari.
Wasu na kiransa da "ɗan gaban goshi" a gwamnatin Bola Ahmed Tinubu. Shi ne babban mashawarci na musamman ga shugaban ƙasa kan harkokin siyasa.
Sai dai ana ganin ƙarfin ikon sa ya wuce na muƙamin da yake riƙewa.
Ibrahim Masari ya riƙe wasu muƙaman siyasa kafin nan, amma sai yanzu ne sunansa ya fi yin amo.
Shin wane irin tasiri yake da shi a gwamnatin APC ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu?

Alhaji Ibrahim Kabiru Masari fitaccen ɗan siyasa ne daga Jihar Katsina, kuma ya yi suna a jam'iyyar APC, musamman saboda kusancinsa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Masari ɗan asalin ƙaramar hukumar Kafur ne da ke Jihar Katsina, kuma yana da alaƙa mai ƙarfi da harkokin siyasar matakin ƙasa da kuma jiha.
Ya fara siyasa ne a ƙarƙashin jam'iyyar PDP a lokacin mulkin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar'Adua.
Bayan haɗewar jam'iyyar CPC da wasu jam'iyyun siyasa da ta haifar da kafa APC a shekarar 2013, Masari na cikin waɗanda suka kafa jam'iyyar.
A wancan lokacin, ya yi aiki tare da tsohon Shugaba Muhammadu Buhari, musamman a lokacin zaɓen 2011.
Daga baya, Masari ya samu ɗaukaka a cikin APC, inda aka naɗa shi sakataren jin daɗi da walwala na ƙasa na jam'iyyar a lokacin da Sanata Adams Oshiomhole ne shugaban APC na ƙasa.
Matsayin ya ƙara masa kusanci da manyan jiga-jigan jam'iyyar da kuma faɗaɗa tasirinsa a harkokin siyasar ƙasa.
Sai dai abin da ya fi ɗaga sunan Ibrahim Masari a siyasar ƙasa shi ne rawar da ya taka a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Alaƙar Masari da Tinubu

Asalin hoton, Alh. Ibrahim Kabir Masari/FB
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Ana kallon Ibrahim Masari a matsayin na kusa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu, kuma ɗaya daga cikin mutanen da ke da tasiri a harkokin APC a matakin ƙasa da ma a Jihar Katsina.
A shekarar 2022, Bola Ahmed Tinubu ya zaɓe shi a matsayin wanda zai tsaya masa a matsayin mataimakin shugaban ƙasa na wucin gadi domin cika wa'adin da hukumar zaɓe ta INEC, ta sanya na gabatar da sunan mataimakin ɗantakarar shugaban ƙasa.
Daga baya Masari ya janye, inda aka maye gurbinsa da Sanata Kashim Shettima, wanda daga bisani ya zama abokin takarar Tinubu a zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Wannan ya ƙara sanya Masari cikin jerin mutanen da aka fi danganta su da alaƙa ta kusa da kuma amincewar Shugaba Tinubu, tare da ƙara masa suna a siyasar ƙasa.
A watan Yulin 2026, Masari ya gabatar da fom ɗin takarar APC, inda aka sake tabbatar da Kashim Shettima a matsayin abokin takarar Tinubu a zaɓen 2027.
Tinubu ya naɗa Masari Babban Mataimaki na Musamman a shekarar 2023, kafin daga bisani ya ƙara masa matsayi zuwa Mai Ba da Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa a ranar 5 ga Maris 2026.
A ranar 22 ga Agustan 2026, an naɗa Masari Mataimakin Darakta-Janar mai kula da dabarun sufuri da ayyuka na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC.
Tasirin Ibrahim Masari a gwamnatin APC

Asalin hoton, Alh. Ibrahim Kabir Masari/FB
Masana harkokin siyasa na cewa Alhaji Ibrahim Kabiru Masari na da matuƙar tasiri a a cikin gwamnatin APC, kuma yana daga cikin amintattun Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Tasirinsa ya ƙara fitowa fili musamman bayan jita-jitar cewa ya taka rawa wajen tsara jerin sunayen kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa na APC na 2027.
Masanin siyasa, Dr Bashiru Ibrahim Kurfi, ya ce Masari na daga cikin mutanen da gwamnatin Tinubu ta fi yarda da su.
Dr Kurfi ya ce tasirin Masari ya wuce yadda mutane da dama suke zato, yana mai cewa matsayinsa na wanda ya tsaya a matsayin mataimakin Tinubu na wucin gadi a zaɓen 2023 ya taimaka wajen ƙara fito da shi fili da kuma ƙarfafa matsayinsa a tsarin siyasar gwamnatin Tinubu.
"Dama duk gwamnatin da ta zo, za ka ga akwai wasu mutane da suke kan gaba, waɗanda suke ƴan gaban goshi saboda amincewar da shugabanni suka yi da su," in ji shi.
Ya ce ana ganin Masari na da ƙarfin zartar da wasu hukunci masu tsauri kuma ana rufe ɗaki da shi domin tattaunawa masu muhimmanci.
Me ƴan APC ke cewa game da Ibrahim Masar?
Wasu 'yan jam'iyyar APC a shafukan sada zumunta sun yi ta nuna rashin jin daɗinsu kan jerin sunayen Kwamitin Yaƙin Neman Zaɓen Shugaban Ƙasa na APC da aka fitar kwanan nan, inda ba a saka Gwamna Radda da wasu na kusa da shi ba. A maimakon haka, jerin ya ƙunshi mutane da ake ganin suna da alaƙa da ɓangaren Masari.
Wasu 'yan jam'iyyar a jihar na kallon hakan a matsayin wani yunƙuri na Masari na ware gwamnan daga tsarin yaƙin neman sake zaɓen Shugaba Tinubu.
Wasu ƙungiyoyin APC na jihar, sun zargi Masari da hannu wajen cire tsohon Ministan Gidaje da Raya Birane, Ahmed Musa Dangiwa, daga mukaminsa.
Wasu kuma na zargin Masari da ƙoƙarin kawar da abokan hamayyarsa na siyasa domin ƙarfafa tasirinsa a jihar Katsina.
Akwai kuma masu ganin cewa Masari da yin wasu "abubuwan da ke kawo cikas ga ci gaban Jihar Katsina, maimakon taimaka mata wajen samun ayyukan gwamnatin tarayya."
Wasu na cewa idan aka bar irin waɗannan abubuwa ba tare da an magance su ba, za su iya janyo wa Shugaba Tinubu koma baya a siyasar Katsina da sauran jihohin Arewa maso Yamma gabanin zaɓen 2027.
Ta kai ta kawo wasu na kira ga Tinubu ya binciki ayyukan Ibrahim Masari.
Me ya haɗa Masari da Gwamna Radda?

Asalin hoton, Alh. Ibrahim Kabir Masari/FB
Ana ganin kamar dangantakar Ibrahim Masari da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda, ta fara tsami, inda aka yi ta ce-ce-ku-ce a cikin jam'iyyar APC, musamman bayan wasu magoya bayan gwamnan sun zargi Masari da amfani da tasirinsa a gwamnatin tarayya wajen ƙoƙarin raunana ikon gwamnan a cikin jam'iyyar jihar.
Bayanai sun ce rikicin ya ƙara ɗaukar sabon salo ne ne bayan Sufeto-Janar na 'Yan Sandan Najeriya ya gayyaci dogarin Gwamna Radda - ADC-, da babban jami'in tsaronsa - CSO - domin yi musu tambayoyi a Abuja.
Wannan mataki ya biyo bayan korafe-korafen lalata wasu allunan tallan siyasa a Katsina da ke ɗauke da hotunan Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Ibrahim Masari inda aka cire Gwamna Radda.
Masanin siyasa Dr Bashiru Ibrahim Kurfi ya shaida wa BBC cewa hakan na daga cikin abubuwan da suka ƙara haifar da rashin jituwar da ake zargin tana tsakanin Masari da Gwamna Radda.
Ya ce lamarin ya ƙara tsananta ne bayan wasu zarge-zargen barazana da tsoratarwa da kuma lalata allunan tallan siyasa, har lamarin ya kai ga gayyatar ADC na gwamnan.
Wannan batu dai ya haifar da rarrabuwar kan ƴan APC na Katsina inda aka samu masu kiran kansu "Katsina APC" da suke tare da Gwamna Radda da "Katsina/Abuja APC" da ta ƙunshi ƴan Katsina masu riƙe da manyan mukamai a gwamnatin tarayya.
Sai dai Daraktan Yaɗa Labarai na Gwamna Radda, Maiwada Danmalam, ya ce bai san da wata rashin jituwa tsakanin gwamnan da Ibrahim Masari ba. Ya shaida wa jaridar Daily Trust cewa shi ma daga wajen ƴan jarida ya fara jin labarin rikicin.











