Ko akwai ƙasar Afirka da za ta iya kai wasan ƙarshe na Kofin Duniya?

Asalin hoton, Getty Images
- Marubuci, Ibrahim Yusuf Mohammed
- Sanya sunan wanda ya rubuta labari, Journalist
- Aiko rahoto daga, Abuja
- An wallafa
- Lokacin karatu: Minti 5
Nahiyar Afirka ta kafa tarihi a gasar cin kofin duniya ta 2026 bayan da ta samu ƙasasheguda 9 da suka tsallaka zuwa zagayen ƴan 32.
Ƙungiyoyin da suka ƙetara daga matakin rukuni su ne Morocco da Afirka ta Kudu da Senegal da Ivory Coast da Ghana da Cape Verde da Masar, DR Congo, da kuma Aljeriya.
Irin rawar da waɗannan ƙasasen na Afirka suka taka ta sake farfaɗo da martabar nahiyar a idon duniya, inda Tunisia ce ƙasa ɗaya tilo da aka fitar daga Afirka a matakin rukunin.
Waɗannan wasannin sun sa manazarta harƙokin wasanni da dama na tambayar ko wane mataki ƙasashen Afirka za su iya kai wa a gasar ta bana?
Tarihin da ƙasashen Afrika suka kafa a gasar bana

Asalin hoton, Getty Images
Morocco ita ce ƙasa ta farko daga Afirka da ta kai wasan kusa da na ƙarshe a gasar cin kofin duniya shekaru huɗu da suka gabata a Qatar, kuma da alama za ta iya sake iya yin nisa a gasar bana, bayan da ta yi kunnen doki da Brazil da ci 1-1 a wasanta na farko a matakin rukuni.
Ta na kuma ɗaya daga cikin masu masaukin baƙi na gasar cin kofin duniya na gaba da za a yi a shekarar 2030.
Ba kowa ne ya yi tunanin cewa 9 daga cikin ƙasashen 10 na Afirka a gasar cin kofin duniya za su samu tikitin zuwa zagayen ƴan 32 ba, amma tawagogin ƙasashen da ke wakilitar nahiyar da dama sun taka rawar gani fiye da yadda ake tsammani kuma sun burge masu bibiyar ƙwallon ƙafa da irin salon wasan da suke takawa.
Wannan babban sauyi ne daga abin da ya faru a Rasha a 2018 lokacin da babu wata ƙasar Afirka da ta tsallaka daga matakin rukuni.
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Masu sharhi kan ƙwallon ƙafa irin su Nazir Jarmajo na ganin cewa ƙarin da aka samu a yawan ƙasashen da ke halartar gasar daga 32 zuwa 48 ya taka muhimmiyar rawa a ƙoƙarin da ƙasashen Afrika suka yi a gasar ta bana.
''Kafin a ƙara yawan kasashen da ke buga wannan gasa, ba a taɓa samun ƙasashe da suka wuce biyu daga nahiyar Afrika da suka tsallaka daga matakin rukuni ba, saboda a baya ƙasashe biyar ne kacal ke zuwa gasar daga nahiyar, yanzu kuma sun kai 10, hakan na nufin damarmaki sun ƙaru, kuma wannan na iya taka rawa a irin nisan da ƙasashen nahiyar za su yi a gasar bana.''
Ƙasashen Afirka shida ne kacal suka taɓa fitowa daga matakin rukuni a tarihin gasar, wasu daga cikinsu fiye da sau ɗaya. Mafi yawa da aka taɓa samu a gasa guda shi ne ƙasashe biyu wanda aka samu a gasannin 2014 da 2022.
Gasar bana dai ta nuna yadda aka samu gagarumin ci gaba a fagen wasan ƙwallon ƙafa a Afirka, inda ƙasashen da ke zuwa gasar a karon farko irinsu Cape Verde da Congo suka samu ƙetarawa zuwa zagayen ƴan 32.
Kongo dai tana da babban aiki a gabanta domin za ta fuskanci Ingila ne a wasanta na gaba.
Yayin da Cape Verde ta burge duniya da sakamakon wasanta na farko a gasar inda ta riƙe Sifaniya 0-0, ba ta kuma yi rashin nasara a duka wasanninta ba.
Maki ukun da ta samu ya ba ta damar kasancewa a matsayi na biyu a rukunin, inda ta shige gaban Uruguay. Amma, Lionel Messi da Argentina ne ke jiran ta a wasanta na gaba.
Wane irin nisa kasashen Afirka za su yi a bana?

Asalin hoton, Getty Images
A zagayen ƴan 32 ƙasashen Afirka za su buga wasu jerin wasanni masu jan hankali amma wanda da ake ganin za su iya zuwa da ƙalubale kamar yadda Afirka ta kudu ta riga ta ɗanɗana bayan an yi waje da ita daga gasar sakamakon kashin da ta sha a hannun mai masaukin baƙi Canada da ci 1-0 .
Morocco wadda ba ta yi rashin nasara a gasar bana ba ya zuwa yanzu za ta kara da Netherlands. Sai kuma Senegal da za ta kara da Belgium, Masar za ta haɗu da Australia yayin da ita kuma Ghana za ta kece raini da Colombia.
Algeria za ta fafata da Switzerland, DR Congo za ta haɗu da Ingila, Ivory Coast kuma za ta fafata da Norway, sai Cape Verde za ta ci gaba da gwagwarmaya a gasar inda za ta sa zare da Argentina mai riƙe da kofin gasar.
Waɗannan jerin wasannin ya sa masharhanta sun fara hasashen matakin da ake ganin ƙasashen Afirka za su iya kai wa a gasar.
Nazir Jarmajo yana ganin bisa la'akari da waɗannan jerin wasannin akwai yiwuwar za a samu ƙasashen nahiyar da za su iya kai labari daga wannan zagayen.
''Akwai yiwuwar za su iya yin nisa a gasar bana idan aka duba irin wasan da suka taka a zagayen rukuni da kuma wasannin da ke gabansu a halin yanzu. Za a iya samun waɗanda za su kai aƙalla zagayen kwata-fainal, idan ma ba su wuce ba, musamman ƙasashe irin su Senegal da Morocco da Ivory Coast ,'' In nji shi.
Mai sharhin ya ƙara da cewa ƙasashe irin su Ghana da Cape Verde da DR Congo sun nuna cewa ba sa fargabar fafatawa da manyan ƙasashen Turai kamar su Ingila da Spain da Portugal.
Ya ce, ''Idan ka yi misali da Ghana, mai horasa da ƴan wasanta gogagge ne a fagen horaswa ganin cewa ya taɓa aiki a Manchester United inda ya nuna cewa yana da ƙwarewa sosai, kuma hakan ya bayyana ƙarara a wasansu da Ingila inda ƴan wasansa suka hana Ingila jefa masu ƙwallo a raga. Ganin irin haka ya sa na ce ƙasahen Afrika na da damar yin nisa a gasar bana.''
Ba a taɓa samun lokacin da Afirka ta shiga zagayen kifa-ɗaya-ƙwala da irin wannan adadi ƙasashen ba, wanda hakan ya bai wa nahiyar damarmaki da dama na samun damar tsallakewa zuwa mataki mai nisa a gasar.
Yayin da a yanzu kowane wasa zai iya kasancewa na ƙarshe ga kowace ƙasa a gasar, wakilan Afirka na da damar sake rubuta sunayensu a cikin littafin tarihin gasar cin kofin duniya.
A yanzu ba a kallon samun gurbi a matakin daf da na kusa da na ƙarshe a matsayin wata babbar nasara amma yanzu ta zame manufa da kowace ƙasar Afirka za ta iya cimmawa, yayin da ake ci gaba da kyautata zato kan yiwuwar samun wata ƙasa daga nahiyar Afirka da za ta iya lashe gasar cin kofin duniya.












