BBC News, Hausa - Labaran Duniya
Babban Labari
KAI TSAYE, 'Duniya za ta fuskanci tsananin yanayin zafi a bana'
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Talata 02/06/2026.
Duk abin da ya kamata ku sani kan Gasar Cin Kofin Duniya ta 2027
Wani babban sauyi da aka samu a gasar ta 2026 shi ne ƙarin yawan ƙasashen da za su fafata zuwa 48.
Nau'in ciwon suga da ke kama siraran mutane
An gano cewa ciwon suga nau'in Type 5 na faruwa ne sanadiyyar tsawon lokaci ba tare da samun abinci mai gina jiki ba, musamman idan mutum ba ya samun ingantaccen abinci na tsawon lokaci ko kuma a lokacin girma. Sai dai har yanzu masana ba su kammala amincewa ko da gaske ciwon na wanzuwa ba ko a'a'.
Manyan sojojin Najeriya biyu da ƴanbidiga suka sace
Sace babban jami'in sojin Najeriya da ya yi murabus, tare da maidakinsa a jihar Katsina da ke arewa maso yammacin Najeriya, ya ƙara jefa fargaba a zuciyar ƴan Najeriya dangane da tsaro.
Sansanonin sojin Amurka 20 da Iran ta lalata
Masana sun shaida wa sashen BBC mai bincike na BBC Verify cewa hare-haren Iran sun yi ɓarna fiye da abin da ya bayyana ga al'umma.
Yadda rikici ya kunno kai a APC a Jigawa
Jam'iyyar ta ce ta dakatar da ɗanmajalisar da ke wakiltar Hadejia da Auyo da Kafin Hausa, a majalisar wakilai ta tarayya, Usman Kamfani Auyo da wasu mutum shida, saboda zargin barazanar yi mata zagon-ƙasa a zaɓe mai zuwa, saboda rashin samun takarar da ɗanmajalisar ya yi.
Iran ta ce ta kai hare-hare kan sansanonin sojin Amurka
Wannan shafi ne da ke kawo muku labarai kan yaƙin Iran da kuma abubuwan da ke faruwa a Najeriya da sauran sassan duniya na ranar Litinin 01/06/2026.
Me ya sa malaman makaranta ke zanga-zanga a jihar Oyo?
Ɗaruruwan malaman makaranta da iyaye da ƙungiyoyin matasa ne suka fantsama kan titunan jihar Oyo domin yin zanga-zanga kan abin da suka kira rashin taɓuka komai daga gwamnati don ceto ɗalibai da wasu malamansu da ƴanbindiga suka sace makwanni biyu da suka gabata.
'Abin da ya sa kakana ya shiga yaƙin Biyafara'
Wani mashiryin fim ɗan Najeriya Meji Alabi ya bayar da umarni wajen haɗa wani muhimmin rahoto na musamman na sashen binciken ƙwaƙwaf na BBC Africa Eye kan yaƙin basasar Najeriya.
Shirye-shiryenmu
Saurari na gaba, Shirin Yamma, 19:29, 2 Yuni 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Rana, 13:59, 2 Yuni 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban-daban na duniya.
Saurari, Shirin Hantsi, 06:30, 2 Yuni 2026, Tsawon lokaci 29,30
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Saurari, Shirin Safe, 05:29, 2 Yuni 2026, Tsawon lokaci 30,00
Shiri ne na minti 30 wanda ya kunshi labaru da rahotanni daga sassa daban na duniya.
Wasanni
KAI TSAYE, Bellingham ne zai sa wa Ingila lamba 10 a gasar kofin duniya
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Litinin 01 zuwa Lahadi 07 ga watan Yunin 2026.
Dokoki 7 da FIFA ta canza a Gasar Kofin Duniya
Ƴan wasa a gasar kofin duniya 2026, za su daina zuwa wajen kociyoyi domin karɓar umarni, da zarar mai tsaron raga ya ji rauni.
Inter Miami na son Guardiola, Silva zai koma Barcelona
Daya daga cikin mutanen da suka mallaki Inter Miami, David Beckham na son ya dauki Pep Guardiola aiki a matsayin sabon kocin kungiyar ta Major League Soccer.
PSG ta shiga jerin manya bayan lashe Champions League na biyu a jere
Paris St-Germain ta kafa tarihin sake lashe Champions League karo na biyu a jere a tarihi, bayan doke Arsenal.
Arsenal ta maza da ta mata na bikin lashe kofuna a bana
Wannan shafi ne da zai ke kawo muku labaran wasannin BBC Hausa daga Litinin 25 zuwa Lahadi 31 ga watan Mayun 2026.
Tashar WhatsApp ta BBC Hausa
A wannan shafin za ku samu labarai daga ƙasashen Afrika da kuma sauran sassan duniya da ɗumi-ɗuminsu domin masu bibiyar mu a WhatsApp.
Kashe ƙwarƙwatar ido
Kuna son tattalin datarku?
Shiga shafinmu na labarai maras hoto domin rage zuƙar data
Labarai da Rahotanni Na Musamman
Ƴan takaran da za su tsaya wa manyan jam'iyyun Najeriya a zaɓen shugaban ƙasa na 2027
Tuni shirye-shiryen zaben suka kankama, inda 'yantakara suka fara tallata kan su domin neman kuri'a.
Yadda ‘yan bindiga suka sace tsohon babban sojan Najeriya da matarsa a Katsina
Ci gaba da irin wannan garkuwa da mutane na nuna karuwar wannan matsala ta rashin tsaro wadda ta addabi arewa maso yammacin Najeriya.
Zafin kaye ne ya sa wasu ke zargin rashin adalci a tsayar da ni takara - MA Abubakar
Tsohon gwamnan jihar Bauchi, kuma dan takarar gwamnan jihar a zaben 2027 da ke tafe Barista Muhammad Abdullahi Abubakar, ya musanta zargin da wasu da suka nemi takarar da shi ke yi na cewa ba a gudanar da zaben cikin gida ba aka tsayar da shi takara.
Ba za mu amince da duk wata yarjejeniya ba sai mun tabbatar za a biya mu diyya - Iran
Wannan shafi ne da kawo muku muhimman bayanan dangane da wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya na ranar Lahadi 31 ga watan Mayun 2026.
Ina Iran ta ɓoye sinadarin Uranium ɗinta na haɗa nukilya?
Shin me ya sa Iran ta adana sinadarin, kuma ina makomar sinadarin?
Yadda takara guda shida da Atiku ya yi a baya suka kasance
A yanzu ya sake samun tikitin takara, wanda wannan ne karo na bakwai da yake takara.
Abun da ya sa muka tsayar da Jonathan takarar shugaban kasa - PDP
Jam'iyyar hamayya ta PDP bangaren Tanimu Turaki, ta bayyana dalilinta na sanar da tsohon Shugaban Kasar, Goodluck Jonathan, a matsayin wanda zai yi mata takarar shugaban kasa a zaben 2027 da ke tafe.
Me ya sauya tun bayan da Tinubu ya karɓi mulkin Najeriya?
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 ne aka rantsar da Tinubu, to amma ana ci gaba da muhawara kan ko Tinubu ya yi wani abin a zo a gani tun daga wancan lokaci.
Wurin da ake tsare masu ƙiba a China
An bayyana wajen rage ƙiba na sojoji wani sansani a China. Wasu na bayana shi da kurkun mas ƙiba, suna fusknatar haramcin cin kai tuya, da cin abinci sau biyu kawai a matsayin jadawalin rage ƙibar.
Abun kunya ne yadda ake ta kashe jama'a a mulkin Abba - Gwarzo
Dan takarar gwamnan Kano a jam'iyyar hamayya ta NDC, kuma tsohon mataimakin gwamnan jihar Aminu Abdussalam Gwarzo, ya caccaki gwamnan jihar Abba Kabir Yusuf, da ya zarga da yin sakaci, wajen kare rayuka da dukiyoyin jama'ar jihar.
'Harin Iran a Kuwait ya jikkata sojojin Amurka da dama'
Wannan shafi ne da kawo muku muhimman bayanan dangane da wainar da ake toyawa a Najeriya da sassan duniya na ranar Asabar 30 ga watan Mayun 2026.
'Tinubu ne ya ƙaƙaba mana ɗan takara a Bauchi'
Yadda zaben fidda gwani na dan takarar gwamna a jihar Bauchi ya bar baya da kura
KAI TSAYE - Labaran BBC Hausa
Saurari labaran BBC Hausa Kai Tsaye Litinin zuwa Juma’a da karfe 0530, 0630, 1400 da 1930 GMT, sai kuma Asabar da Lahadi da karfe 0530, 0630 da 1930 GMT.






























































