Mece ce makomar Jami'ar Jihar Kaduna bayan malamai fiye da 200 sun bar ta?

An wallafa
Lokacin karatu: Minti 5

Wani jawabin da shugaban ƙungiyar Malaman Jami'a ta Najeriya, ASUU, reshen jihar Kaduna ya yi kan yawan malaman da suka bar jami'ar ya ɗauki hankalin ƴan Najeriya.

Cikin jawabin da ya gabatar a wani taron manema labarai, shugaban na ASUU reshen KASU, Dr Abubakar Abdullahi ya ce kimanin malaman jami'ar 200 ne suka daina aiki a cikinta, sakamakon abin da ya bayyana da rashin ingancin walwalar malaman.

Dr Abdullahi ya ce malaman da suka bar jami'ar sun haɗa da manyan malamai, ciki har da farfesoshi, lamarin da ya bayyana a matsayin babbar barazana ga ingancin koyarwa da bincike da ci gaban jami'ar gaba ɗaya.

ASUU ta danganta ajiye aikin malaman da abin da ta kira rashin kyawun walwala da kuma gazawar gwamnatin jihar Kaduna wajen aiwatar da wasu yarjejeniyoyi da suka shafi jin daɗin ma'aikata.

Dr Abdullahi, ya ce rashin aiwatar da yarjejeniyar da ƙungiyar ta cimma da gwamnatin tarayya a 2025 ne ya sa malamai da dama suka nemi guraben aiki a wasu jami'o'i da cibiyoyin ilimi da ke ba da yanayin aiki mai kyau da ƙarin albashi.

Masana ilimi sun ce barin ɗimbin malamai daga jami'ar na iya haifar da ƙarancin ƙwararrun ma'aikata da jinkirin gudanar da ayyukan ilimi da bincike da kuma ƙarin nauyi ga malaman da suka rage.

Waɗanne yarjejeniyoyi ne?

A hirarsa da BBC shugaban na ASUU reshen jami'ar, Dr Abubakar Abdullahi ya ce yarjejeniyoyin da aka cimma tsakanin gwamnati da ƙungiyar sun ƙunshi na walwalar malaman da kuɗaɗen gudanarwar makarantu.

''Yarjejeniyoyi ne suka ƙunshi kuɗaɗen gudanarwa da sauran haƙƙokin malamai ciki har da albashinsu'', in ji shi.

Dr Abdullahi ya ce tun bayan cimma waɗannan yarjejeniyoyi da gwamnatin tarayya, jami'o'i da dama na gwamnatin tarayya da na wasu jihohin sun fara amfana.

''Amma har yanzu jami'ar jihar Kaduna ba a fara amfana daga yarjejeniyar ba'', kamar yadda ya yi iƙirari.

Ya ƙara da cewa yarjejeniyar ta ƙunshi ƴancin cin gashin kan jami'o'i.

Dr Abdullahi ya ce rashin aiwatar da yarjejeniyar ya jefa rayuwar malaman jami'ar cikin mawuyacin halin tattalin arziki.

Malamai nawa ne suka bar jami'ar KASU?

Dr Abdullahi ya ce rashin aiwatar da wannan yarjejeniya ya jefa jami'ar jihar Kaduna cikin mawuyacin hali, lamarin da ya sa wasu daga cikin malaman jami'ar suka bar aiki a jami'ar.

''Wannan al'amari ya tailasta wa malaman jami'ar jihar Kaduna kimanin 200 barin aiki a jami'ar, saboda matsin tattalin arziƙi da suka shiga sakamakon rashin aiwatar da yarjejeniyar,'' kamar yadda ya shaida wa BBC.

Dr Abdullahi ya ce a yanzu malaman jami'ar da dama ba su iya ɗaukar ɗawainiyar sufurunsu domin zuwa wurin aiki.

''Na san malaman da ko kuɗin sanya mai a baburansu, ba su da shi, saboda ƙarancin albashin da ake biyan su'', in ji shi.

Wane hali jami'ar ta shiga?

Dr Abdullahin ya ce jami'ar ta shiga halin rashin ƙwararrun malamai, lamarin da ke barazana ga cigaban jami'ar.

''Shi ɓangaren ilimi ana buƙatar ƙwararrun masana da za su jajirce wajen tafiyar da ɓangaren, don haka tafiyar irin waɗannan malaman ya shafi harkokin ingancin koyarwa a jami'ar'', in ji shi.

Shugaban na ASUU ya ce hakan ba ƙaramar asara ba ce ga gwamnatin jihar da kuma jami'ar, saboda hakan koma-baya ne gare ta.

''A ƙa'idar jami'a shi ne yawan malaman da kake da shi ne zai yanke hukuncin yawan ɗaliban da jami'a za ta ɗauka, to in malamai na raguwa ai hakan zai shafi ingancin koyarwa a jami'ar'', in ji shi.

Mece ce buƙatar malaman KASU?

Dr Abdullahi ya ce babban abin da ƙungiyarsu ke buƙata daga ɓangaren gwamnatin jihar Kaduna shi ne aiwatar da yarjejeniyar da aka sanya wa hannu.

''Hakan ne zai sa malamai su samu albashi mai inganci, su kuma gudanar da ayyukansu yadda ya kamata ba tare da matsi ba'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa idan hakan ta faru malaman jami'ar za su samu nutsuwar gudanar da ayyukansu.

Haka kuma shugaban na ASUU ya ce ƙungiyarsu na buƙatar gwamnatin jihar Kaduna ta bai wa jami'ar kuɗaɗen da suka kamata domin aiwatar da harkokinta.

''Sannan muna buƙatar gwamnati ta bai wa jami'ar ƴancin cin gashin kanta, wajen aiwatar da ayyukanta da take son gudanarwa a harabar jami'ar'', in ji shi.

Malaman da suka ajiye aiki cikin shekaru 3 ba su wuce 50 ba - Gwamnatin Kaduna

Gwamnatin Jihar Kaduna ta yi ƙarin bayani kan turka-turkar da ake yi tsakaninta da malaman Jami'ar Jihar, KASU, bayan da ƙungiyar malaman jami'o'i ta ASUU ta yi iƙirarin cewa sama da malamai 200 sun ajiye aikinsu saboda rashin kyawawan yanayin aiki.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Ahmed Maiyaki, ya shaida wa BBC cewa rahotannin da ASUU ke yaɗawa ba gaskiya ba ne.

Ya ce gwamnatin jihar ta yi iya bakin ƙoƙarinta wajen biyan da dama daga cikin buƙatun malaman cikin sama da shekaru ukun da ta yi tana mulki.

Ya ce yawan waɗanda ake cewa sun ajiye aiki bai wuce mutum 50 ba cikin shekaru ukun da gwamnatin ta yi, kuma mafi yawansu sun samu sauyin wurin aiki ne, ba wai saboda rashin jin daɗin yanayin aiki ba.

Kwamishinan ya ƙara da cewa gwamnati na tattaunawa da malaman jami'ar domin lalubo mafita kan matsalolin da suka taso.

Martanin KASU

Shugaban Jami'ar Jihar Kaduna (KASU), Farfesa Ibrahim Musa, ya musanta ikirarin da ASUU ta yi cewa malamai sama da 200 sun yi murabus daga jami'ar, yana mai cewa wannan ikirari ya saɓa wa bayanan da jami'ar ke da su.

A cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, Farfesa Musa ya ce ASUU ta ƙirƙiro alkaluma ne kawai, yana mai jaddada cewa jama'a su yi watsi da wannan ikirari.

Ya bayyana cewa sauye-sauyen ma'aikata sakamakon murabus, ritaya, canjin aiki ko neman wasu damammakin sana'a abu ne na yau da kullum a tsarin jami'o'i, don haka bai kamata a riƙa gabatar da su ba tare da cikakken bayani ba a matsayin hujjar cewa yanayin aiki ya tabarbare a jami'ar.

Haka kuma, ya ƙalubalanci ASUU da ta gabatar da hujjoji masu inganci, ciki har da sunayen waɗanda ake zargin sun yi murabus, kwanakin da suka yi murabus da kuma dalilan da suka sa suka bar Jami'ar Jihar Kaduna.

Shugaban jami'ar ya ce gwamnatin Uba Sani ta fitar da sama da Naira miliyan 800 domin jin daɗin ma'aikata cikin shekaru uku, baya ga Naira miliyan 146 da aka yi amfani da su wajen biyan wasu bashin albashi da alawus-alawus da aka gada daga gwamnatocin baya.

Ya kuma ce gwamnati, jami'ar da ƙungiyar ASUU sun kafa wani tsarin tallafi na Naira miliyan 50 a kowane wata domin taimaka wa jami'ar.

"A shekarar 2026 kaɗai kuma, an samar da sama da Naira miliyan 200 domin gudanar da ayyukan jami'ar, ciki har da kayan gwaje-gwaje, tafiye-tafiyen ɗalibai da jarabawa", in ji shi.

Sai dai duk da haka shugaban jami'ar ya amince cewa har yanzu akwai wasu buƙatun ma'aikata da ba a warware su ba, amma jami'ar na aiki da gwamnati domin magance su a hankali.

ASUU dai ta ce matsalar ta samo asali ne daga rashin aiwatar da yarjejeniyar da gwamnatin tarayya da ƙungiyar suka cimma a shekarar 2025.

Wace illa barin malaman zai yi wa jami'ar?

Dr Abdurrazak Ibrahim malami a Jami'ar North West da ke Kano, masanin harkokin koyo da koyarwar jami'o'i ya ce halin da Jami'ar jihar Kaduna ke ciki, yana buƙatar ɗaukar mataki.

''Bai kamata a bari Jami'ar Kaduna ta zama haka ba, domin jami'ar ita ce ta farko mallakin gwamnatin jiha a arewacin Najeriya, don haka bai kamata a bari ta shiga wannan hali ba'', in ji shi.

Masanin ya ce idan aka bari al'amura suka ci gaba da tafiya a haka a jami'ar Kaduna to komai zai iya taɓarɓarewa a jami'ar.

Ya ci gaba da cewa barin jami'a ga malamanta ba ƙaramar barazana ba ce, ga ci gaba da wanzuwarta.

''Ƙwararrun malamai ne da suka jima suna koyarwa shekara da shekaru, don haka rasa su ba ƙaramar illa ba ce ga jami'ar'', in ji shi.

Ya ƙara da cewa matsawar ba a magance wannan matsala ba, to za a iya rufe Jami'ar KASU.