Wane ne Abu Musa Al-Mangawi, gwamnan ISWAP da sojojin Najeriya ke nema ruwa a jallo?

Asalin hoton, HQ Nigerian Army
Sojojin Najeriya sun bayyana Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa a matsayin jagoran ƙungiyar ISWAP (Islamic State West Africa Province) da ake nema ruwa a jallo a yankin Tafkin Chadi, tare da sanar da cewa za su ba duk wanda ya bayar da sahihin bayanin da zai kai ga kama shi tukuici mai tsoka.
A cikin wata sanarwa da Operation HADIN KAI ta fitar, rundunar ta ce duk wanda ya bayar da ingantaccen bayani da zai taimaka wajen kama Al-Mangawi zai samu lada mai yawa, yayin da za a kare sunansa da bayanansa cikin sirri.
Sanarwar ta biyo bayan hare-haren da sojoji suka kai kan mayakan ISWAP a arewacin jihar Borno, inda suka ƙwace kyamarori, na'urorin sadarwa da sauran muhimman kayayyakin leƙen asiri.
A cewar rundunar, binciken da masana suka yi kan na'urorin ya taimaka wajen gano sunayen manyan shugabannin ISWAP da wuraren da suke gudanar da ayyukansu.
Yadda sojoji suka gano shugabannin
Operation HADIN KAI ta ce dakarunta sun ƙwace kyamara ta bidiyo (camcorder) da wasu muhimman na'urori da mayakan ISWAP ke amfani da su wajen ɗaukar bidiyoyin farfaganda da kuma rubuta ayyukan hare-harensu.
Bayan binciken ƙwararru kan waɗannan na'urori, an samu bayanan sirri da suka taimaka wajen gano sansanonin 'yan ƙungiyar da kuma manyan shugabanninsu da ke aiki a yankin Mangari–Metele–Dogon Chukun, kusa da Tafkin Chadi, a ƙananan hukumomin Abadam da Kukawa na jihar Borno.
Sojojin sun bayyana sunayen wasu daga cikin manyan shugabannin da suka gano, waɗanda suka haɗa da:
- Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa – Wali (Gwamnan ISWAP).
- Muhammad Jidda, wanda aka fi sani da "Mai hannu ɗaya", mataimakin Wali kuma Amirul Jaish.
- Hamad Abu Hanifa – Amirul-Fiya na ISWAP.
- Ibn Muhammad – shugaban sashen Amniya, wato bangaren leƙen asiri da tsaro na ƙungiyar.
Rundunar ta kuma fitar da hotunan waɗannan shugabanni domin taimakawa jama'a wajen gane su.
Wane ne Abu Musa Al-Mangawi?

Asalin hoton, Getty Images
A cewar sojojin Najeriya, Abu Musa Al-Mangawi Baa Shuwa shi ne Wali, wato babban shugaban ISWAP a yankin Afirka ta Yamma.
A tsarin shugabancin ISWAP, mukamin Wali shi ne mafi girma, kuma mai riƙe da shi ne ke kula da jagorancin yaƙi, tafiyar da harkokin ƙungiyar da kuma yanke manyan shawarwari.
Rahotannin sojoji sun nuna cewa Al-Mangawi na jagorantar mayakan ISWAP da ke aiki a yankin Tafkin Chadi, musamman a wasu sassan arewacin Borno.
Bayyana shi a matsayin mutumin da ake nema ruwa a jallo ya nuna cewa hukumomin tsaro na kallonsa a matsayin ɗaya daga cikin manyan shugabannin ISWAP da suka rage bayan shekaru na farmakin sojoji kan ƙungiyar.
Me ya sa ake nema ruwa a jallo?
Operation HADIN KAI ta ce Abu Musa Al-Mangawi shi ne jagoran ISWAP da ake nema ruwa a jallo fiye da kowa a yankin Tafkin Chadi.
Rundunar ta ce bayanan da aka samu daga na'urorin da aka ƙwace sun ba ta damar gano hanyoyin sadarwarsa, inda yake aiki da kuma wasu daga cikin mutane na kusa da shi.
Saboda haka ne sojoji suka yanke shawarar neman haɗin kan jama'a domin samun ƙarin bayanan sirri da za su taimaka wajen kama shi.
Sun kuma tabbatar da cewa za a kare bayanan duk wanda ya bayar da sahihin bayani.
Nawa ne tukuicin?
Sojojin Najeriya sun sanya tukuici daban-daban kan wasu daga cikin shugabannin ISWAP.
Sun haɗa da:
Tukuici mai yawa ga duk wanda bayaninsa ya kai ga kama Abu Musa Al-Mangawi.
- Naira miliyan 50 ga duk wanda ya bayar da bayanin da zai kai ga kama Ibn Muhammad, shugaban sashen Amniya na ISWAP.
- Naira miliyan 10 ga bayanin da zai kai ga kama Muhammad Jidda, wanda aka fi sani da "Mai hannu ɗaya".
- Rundunar ta ce akwai wasu manyan shugabannin ISWAP da ma aka saka a cikin jerin mutanen da ake nema.
Me hakan ke nufi?
Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.
Latsa nan domin shiga
Karshen Whatsapp
Operation HADIN KAI ta roƙi jama'a su taimaka wa jami'an tsaro ta hanyar bayar da sahihan bayanai, amma ta yi gargaɗin kada wani ya yi yunƙurin kama ko tunkarar waɗannan mutane saboda haɗarin da ke tattare da hakan.
A maimakon haka, ta buƙaci duk wanda ke da wani bayani ya kai shi ta hanyoyin da hukumomin tsaro suka tanada.
Sanarwar ta ce: "Za a kula da duk bayanan da aka bayar cikin cikakken sirri, kuma za a kare bayanan masu bayar da rahoto."
Bayyana Abu Musa Al-Mangawi a matsayin shugaban ISWAP da ake nema ruwa a jallo fiye da kowa na nuna irin muhimmancin da hukumomin tsaro ke bai wa rusa ragowar shugabancin ƙungiyar a yankin Tafkin Chadi.
A cikin ƴan watannin nan, Operation HADIN KAI ta ƙara kaimi wajen kai hare-hare kan ISWAP da Boko Haram, inda ta ce ta kashe tare da kama wasu manyan shugabannin ƙungiyoyin tare da lalata sansanoninsu.
Ta hanyar haɗa hare-haren soji da kuma bayanan sirri daga jama'a, hukumomin tsaro na fatan ƙara raunana tsarin jagorancin ISWAP da hana ta ci gaba da kai hare-hare a arewa maso gabashin Najeriya.











