Arsenal da Man Utd na sa ido kan Elias, Juve za ta karɓi aron Zirkzee

Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ba ta niyyar ɗauko ɗanwasan baya na Tottenham da Ingila Djed Spence, mai shekara 25, wanda ke yawan zuwa jinyar rauni. (Mirror)
Juventus na koƙarin karɓo aron ɗanwasan gaba na Joshua Zirkzee, mai shekara 25, ba tare da sharaɗin sayen ɗanwasan na Manchester United ba. (Gazzetta dello Sport - in Italian)
Arsenal da Manchester United sun tura wakilai domin sa ido kan ɗanwasan gaba Kaua Elias mai shekara 20 wanda ya zura wa Shakhtar Donetsk kwallaye uku rigis a wasannin share fagen kaka, yayin da AC Milan da Porto ke son ɗanwasan na Brazil. (Sun)
Liverpool ta tsananta tattaunawa da wakilan matashin ɗanwasan Paris St-Germain da Senegal Ibrahim Mbaye bayan ɗanwasan ya nuna yana son barin ƙungiyar. (Teamtalk)
An dakatar da tattaunawa tsakanin West Ham da Tottenham kan ɗanwasan gaba na Isra'ila Manor Solomon saboda dalilai na kuɗi, yayin da West Ham ta nuna ba ta iya biyan kuɗaɗen lada da Spurs ke buƙata idan har ta dawo gasar Premier League. (Athletic - subscription required)
Ipswich da Everton na cikin ƙungiyoyin da ke son ɗanwasan Senegal Krepin Diatta, wanda kwangilar shi ta kawo ƙarshe a Monaco a wtaan Yuni. (Footmercato - in French)
Ipswich na ci gaba da tattaunawa da Fulham domin sayen ɗanwasan tsakiya na Serbia Sasa Lukic. (Sky Sports)
Galatasaray ta kara sunan ɗanwasan gaba na Arsenal da Brazil Gabriel Martinelli cikin lissafin ƴanwasan da take farauta. (Gianlucadimarzio - in Italian)











