'Yadda na tsere na bar matata da tagwayen ƴaƴana a Afirka ta Kudu'

Ɗan Najeriyar da ya tsere daga Afrika ta Kudu ya bar matarsa da ƴaƴansa biyu

Asalin hoton, BBC/Gift Ufuoma

Bayanan hoto, Richard Itoro
    • Marubuci, Makuochi Okafor
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Lagos
    • Marubuci, Thomas Naadi
    • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC Africa
    • Aiko rahoto daga, Accra
  • An wallafa
  • Lokacin karatu: Minti 6

Richard Itoro, ɗan Najeriya ne mai shekara 47, ya ce bai san lokacin da zai sake ganin tagwayen ƴaƴansa ba.

Sakamakon fargabar rashin tsaro yayin da zanga-zangar adawa da baƙin haure ta yi ƙamari a Afirka ta Kudu a bana, ya bar matarsa da kasuwancinsa a birnin Johannesburg, sannan ya hau ɗaya daga cikin jiragen da suka koma da ƴan ƙasarsa Najeriya a watan Yuni.

Labarinsa na ɗaya daga cikin labaran da ke ƙara haifar da zaman ɗar-ɗar ta diflomasiyya tare da barazana ga dangantakar Afirka ta Kudu da wasu ƙasashen nahiyar.

A cikin watanni biyu da suka gabata, dubban baƙi ne suka bar ƙasar.

"Akwai matuƙar raɗaɗi na bar wadda ita ce babbar aminiya ta," in ji Itoro cikin hawaye yake wannan bayani yayin da yake tuna ranar da ya yi bankwana da matarsa ƴar Afirka ta Kudu.

A tsawon shekaru 15 da ya yi a ƙasar, ya gina kasuwancin sayar da motoci, ya mallaki gida kuma yana da iyali. Amma yanzu, a cewarsa, ya rasa komai.

Itoro ya ce ana yawan tsangwamarsa da matarsa saboda asalinsa na ɗan Najeriya.

Ya ce maƙwabtansu sun gaya wa matarsa: "Kin auri ɗan Najeriya. Ku ma waɗanda kuka auri ƴan Najeriya ya kamata a kama ku. Kun ci amanarmu. Ku bar ƙasar tare da mijinki."

Ya ce har yanzu bai fahimci dalilin da ya sa aka yi musu haka ba.

"Ban tara iyali da yawa ba, kuma muna zaune cikin kwanciyar hankali. Ban taɓa samun matsala da kowa ba."

Daga ƙarshe, ya ce matsin lambar ya yi yawa har ya ga gara ya koma Najeriya ya fara rayuwa daga farko fiye da ya ci gaba da zama cikin tsoro da fargabar rasa ransa.

Zanga-zangar kira ga baƙin hauren da ba su da takardun zama su fice daga ƙasar a ƙarshen watan Yuni

Asalin hoton, Gallo Images via Getty Images

Bayanan hoto, Zanga-zangar kira ga baƙin hauren da ba su da takardun zama su fice daga ƙasar a ƙarshen watan Yuni
Tsallake Whatsapp
Tasharmu ta WhatsApp

Yanzu za ku iya samun labaran BBC Hausa kai-tsaye a wayoyinku.

Latsa nan domin shiga

Karshen Whatsapp

Sai dai Itoro ya ce ofishin jakadancin Najeriya da ke Afirka ta Kudu bai ba matarsa da ƴaƴansa damar tafiya tare da shi zuwa Najeriya ba.

Ya ce yana ganin kamar a fim, inda mutum ke hawa jirgin ƙarshe domin tserewa daga wani birni da aka yi wa ƙawanya.

"Na so a ce zan iya roƙon jami'an ofishin jakadancin na ce musu, 'Ga matata nan, ba zan iya barinta tare da ƴaƴana ba.' Amma ban samu damar yin hakan ba."

"Bayan da motar ta fara tafiya, abin da nake fata kawai shi ne da na ce mata kada ta yi kuka."

Ƙungiyoyin da suka jagoranci zanga-zangar ƙyamar baƙi a Afirka ta Kudu sun ce manufarsu ita ce korar baƙin da ba su da takardun zama a hukumance. Ministan Al'adu na ƙasar, Gayton McKenzie, wanda ke jagorantar ɗaya daga cikin jam'iyyun da ke cikin gwamnatin haɗaka, shi ma ya nanata wannan matsaya.

"Muna faɗin cewa Afirka ta Kudu a buɗe take ga ƴan'uwanmu na nahiyar Afrika, amma su shigo bisa tsarin doka. Su zo da takardunsu," kamar yadda ya shaida wa BBC.

Sai dai Itoro ya ce duk da kasancewarsa ɗan ƙasar waje mai takardun zama a hukumance, hakan bai hana a ci gaba da yi masa barazana ba. Ya kuma nuna wa BBC takardar da ya ce ta tabbatar yana da izinin zama a ƙasar.

A cewarsa, ba shi kaɗai ne ya fuskanci irin hakan ba.

Ministan Ƙaramin Harkokin Wajen Najeriya, Sola Enikanolaiye, ya shaida wa takwaransa na Afirka ta Kudu, Ronald Lamola, cewa: "Muna da bayanan ƴan Najeriya da ke da takardun zama a Afirka ta Kudu, amma duk da haka an kai musu hare-hare."

Takun-saƙar ta ƙara ƙamari a makon da ya gabata bayan mutuwar wani ɗan Najeriya da aka kashe yayin da ƴan sanda ke ƙoƙarin kama shi bisa zargin safarar miyagun ƙwayoyi. A yanzu haka wani kwamiti mai zaman kansa na binciken lamarin.

Sai dai Lamola, ya ce gwamnati na hukunta duk wanda ya ɗauki doka a hannunsa, kuma Shugaba Cyril Ramaphosa ya jaddada cewa Afirka ta Kudu na da cikakken ikon aiwatar da dokokinta na shige da fice.

Ghanaian Emmanuel Asamoah
Bayanan hoto, Ghanaian Emmanuel Asamoah

Duk da ƙoƙarin diflomasiyya da ake yi, martabar Afirka ta Kudu ta yi rauni a idon duniya.

Hakan ya ƙara tsanani ne sakamakon hotuna da bidiyoyin da suka yaɗu a kafafen sada zumunta. Duk da cewa ba dukkansu ne na gaskiya ba, amma wani bidiyo da ya shafi wani ɗan Ghana ya tayar da hankula sosai bayan ya yaɗu a watan Afrilu.

Lokacin da Emmanuel Asamoah ya bar Ghana zuwa Afirka ta Kudu a shekarar 2023, burinsa shi ne samun damar rayuwa da aiki kamar yadda yawancin baƙin haure ke fata.

Yana sana'ar gyaran gashi kuma yana da shekara 37. Ya zauna a Soweto da ke wajen birnin Johannesburg, ya samu aiki, yana gina rayuwarsa, kuma ya yi imanin cewa yana da makoma mai kyau ƙasar.

Sai dai watanni uku da suka gabata rayuwarsa ta sauya, bayan wasu ƴan Afirka ta Kudu sun kewaye shi suna neman ya bar ƙasar. An ɗauki bidiyon wannan taƙaddamar.

A cikin bidiyon, an ji wata mata tana cewa: "Wannan abin da kuke yi na barin wata ƙasa zuwa wata ya ƙare. Muna so ku bar nan. Ku koma ku gyara ƙasashenku."

Asamoah, wanda ya koma Accra babban birnin Ghana a watan Mayu, ya shaida wa BBC cewa abin ya firgita shi matuƙa.

"Sun zo suka fara tura ni... suna yi min tambayoyi tare da muzgunawa. Suka ce in koma ƙasata, suna zargin mu ne muka lalata ƙasarsu, saboda mu ba sa samun abinci, kuma muna ƙwace musu ƴan mata," in ji shi.

Masana na ganin yawan rashin aikin yi a Afirka ta Kudu, wanda ya haura kashi 30, na ɗaya daga cikin manyan abubuwan da ke haddasa wannan tashin hankali. Wannan shi ne ra'ayin da Ministan Al'adu na ƙasar, Gayton McKenzie, ya bayyana.

"Babu mutumin da zai ciyar da ƴaƴan wani alhali nashi na fama da yunwa. Mutanenmu na fama da rashin aikin yi," in ji shi, inda yake goyon bayan kira ga baƙin hauren da ba su da takardun zama su fice daga ƙasar.

.....

Asalin hoton, Gallo Images via Getty Images

Sai dai Asamoah ya ce yana da sahihan takardun zama a Afirka ta Kudu, wadda aka buga masa a fasfo dinsa.

"Ba bisa ƙa'ida ba ne nake zaune. Ina da sahihiyar takardar zama a Afirka ta Kudu. Shi ya sa na ce musu su kai ni ofishin ƴan sanda, daga nan kuma mu je Hukumar Shige da Fice domin a tabbatar da hakan," in ji shi.

Komawarsa Ghana kuwa ta zama wata sabuwar dama a rayuwarsa.

Da taimakon wani ɗan kasuwa ɗan Ghana, ya buɗe kasuwancin siminti, kuma ya ce ya ƙuduri aniyar gina makomarsa a ƙasarsa.

"Ina sanar da ƴan'uwana maza da mata a Afirka ta Kudu ce yanzu ina Ghana, kuma ina gyara ƙasata," in ji shi.

Sai dai gwamnatin Ghana ta nuna fushinta kan yadda take ganin ana mu'amala da ƴan ƙasar a Afirka ta Kudu.

A wata hira da BBC, Ministan Harkokin Wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ya ce abin da ke faruwa ya saɓa wa fatan haɗin kan ƙasashen Afirka, kuma ya yi watsi da irin gudunmawar da ƙasashen nahiyar suka bayar a yaƙin kawo ƙarshen wariyar launin fata a Afirka ta Kudu a shekarar 1994.

Ya ce: "Ya kamata Afirka ta Kudu ta kasance abin koyi wajen nuna soyayyar Afrika. Muna magana ne kan haɗin kan Afirka da kuma ƴancin zirga-zirga. Ko da kuna da matsalar yawan baƙin haure, shin haka ya kamata a magance ta?"

A birnin Legas kuwa, Richard Itoro har yanzu na kewar matarsa da ƴaƴansa.

"Ba abu ne mai sauƙi ba. Amma muna magana kullum, kuma zuciyata ta karaya. Ina fatan matata za ta zo ta haɗu da ni nan ba da jimawa ba idan Allah Ya sauƙaƙa. Amma abin ya yi mini ciwo sosai, na ji kamar na rasa komai."

Ƙarin rahotanni daga Abayomi Adisa